An Shiga Tashin Hankali: Girgizar Kasa Mai Girma Ta Afku a Jamhuriyar Musulunci ta Iran
- Girgizar kasa mai karfin maki 5.0 ta afku a yankin Saland na lardin Khuzestan a Iran wanda ya tayar da hankula
- Majiyoyi sun tabbatar da cewa jami'an ceto suka garzaya domin tantance barnar da ta faru wanda mutane da dama suka jikkata
- Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da rikicin soji tsakanin Iran da Amurka ke kara kamari, inda bangarorin biyu ke ci gaba da musayar hare-hare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Khuzestan, Iran - An shiga tashin hankali a kasar Iran bayan iftila'in girgizar ƙasa da ya tayar da hankula.
Girgizar kasar mai karfin maki 5.0 ta afku a yankin Saland na lardin Khuzestan da ke kudu maso yammacin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Source: Getty Images
Rahotannin kafafen gwamnatin Iran sun ce girgizar ta faru ne a zurfin kusan kilomita 12, cewar rahoton Al Jazeera.
Kokarin da ƙungiyoyin agaji ke yi a Iran
Kungiyar agajin gaggawa ta Red Crescent ta Iran ta sanar da cewa ta tura tawagogin ceto biyu zuwa kauyukan da ke kusa da cibiyar girgizar, manufar hakan ita ce tantance ko an samu barna.
Lamarin ya tayar da hankula tare da jefa fargaba a zukatan mutanen yankin saboda rashin sanin hakikanin barnar da hakan ya jawo, cewar Middle East Eye.
Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, hukumomi ba su kai ga fitar da sanarwa ba domin fayyace irin barnar da girgizar kasar ta yi.
Wannan girgizar kasa ta afku ne yayin da rikicin soji tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da tsananta bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta rushe mako guda da ya gabata.
Rahotanni sun ce dakarun Amurka sun ci gaba da kai hare-hare kan wurare a Iran, a nata bangaren, Iran ta kai farmaki kan sansanonin sojin Amurka da ke yankin Tekun Gulf.

Source: Getty Images
Yadda aka kashe sojojin Amurka a Jordan
A wani hari da Iran ta kai kan sansanin Amurka da ke Jordan, an kashe sojojin Amurka biyu, yayin da aka bayyana cewa wani soja guda ya bace.
Iran na cikin kasashen duniya da girgizar kasa ke yawan afkuwa saboda tana kan iyakar haduwar farantan nahiyoyin Larabawa da Eurasia, wadanda ke ci gaba da motsi.
Masana sun bayyana cewa girgizar kasa mai zurfi kadan na iya haddasa girgiza mai karfi da barna, musamman a yankunan da jama'a ke da yawa.
A watan Yunin 2026 ma, an samu wata girgizar kasa mai karfin maki 5.0 a lardin Hormozgan. Sai dai jami'ai sun ce ba a samu asarar rayuka ko gagarumar barna ba.
Iran: Girgizar kasa ta afkawa birnin Tehran
A wani labari mai kama da wannan, an ji cewa hukumomi a Jamhuriyar Iran sun tabbatar da samun girgizar kasa mai karfin maki 4.6 ta afku kusa da Tehran a kasar.
Hukumar binciken girgizar kasa ta Iran ta bayyana cewa girgizar ta auku ne kusa da iyakar Tehran da Mazandaran.
Rahotanni sun ce an ji girgizar a wasu yankuna da birane makwabta, amma har yanzu ba a samu bayanan asarar rayuka ba.
Asali: Legit.ng

