Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri

Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri

- Kasar Misra, Egypt, na daga cikin kasashen duniya masu tsohon tarihi, dalolinsu na duwatsu kaburbura ne domin firaunonisu na zamunna da dama

- Masu yawon bude ido na tururuwar zuwa kasar Misra, wuraren tarihi da dama a ffadin kasar, wasu sum kai shekaru 5,000

- A kasar Misra fadar Fira'aunonin take, kuma banda na annabi Musa da Yusufu, anyi fir'aunoni da dama a tsahon daular dadaddiya, wadda ke da ababen bauta da yawa

Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri
Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri

Dalar tsandauri na kasar Misra na daya daga cikin gine-ginen duniya masu dumbin tarihi. Dalar tsandaurin, na daga wajen babban birnin kasar Misra, Alqahira, wato Cairo.

Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri
Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri

Dalar tsandauri na kasar Misra na daga cikin ragowar abubuwan al'ajabi guda bakwai da duniya ta gada daga magabata.

Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri
Dalar tsandauri ta Misra

An fara gina Dalar tsandauri a kasar Misra a shekarar 2551 kafin zuwan Annabi Isa a garin Giza, a karkashin mulkin sarkin Misra Fira'auna Khufu. Dalar Giza nada tsawon kafa 455, kilomita 138, kuma ana yi ma ta kirari da cewar "Dala mai girma", da ta kasance daya daga cikin abin al'ajabi bakwai da har yanzu duniya ke mamaki.

Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri
Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri

Dalar tsandaurin ta samo asali ne daga sana'ar fasa duwatsu a kudu maso gabashin birnin Misra. Cikin Dalar na dauke da adon farin dutse.

Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri
Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri

DUBA WANNAN: Kashi na biyu: Dubi hotunan Bishiyoyi masu abin al'ajabi

Saida aka shude tsawon shekaru 20 kafin mutanen kasar Misra na wancan lokacin su gina Dala guda daya. Kuma wani abin mamaki da wadannan Dala na kasar Misra shi ne; har yanzu, duk da yawaitar ilimin kimiyya da fasaha, ba a gano irin fasahar da mutanen wancan lokaci suka yi amfani da ita wajen yin wadannan manya-manyan gini ba.

Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri
Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri

Ana dai hasashen sun kera su ne da gara kowanne bulo mai nauyin tan 2, na dutse, kan gare-gare na icce har sama, ko kuma dorawa kan yashi, daga baya a zaizaye yashin ta karkashi.

Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri
Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri

Bayi ne ke wannan aiki, da leburori, kuma fir'aunonin kan fito don duba yadda ake aikin makwancinsu bayan sun mutu.

Dalar tsandauri ta kasar Misra
Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri

Tarihi ya nuna cewar ana amfani da cikin Dalar ne a matsayin wurin zaman taro na musamman a wancan lokacin, dalilin da yasa ciki Dalar ake ganin duwatsu da aka kankare su ya zuwa fasalin bencin zama.

Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri
Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri

Mayatar firaunonin ta son sake rayuwa bayan mutuwa da ci gaba da mulki, domin jama'arsu da bokayensu sun Allantar dasu, tasa suke gina wadannan daloli a matsayin kabari, dauke da dawaki, dakuna, da kayan abinci da gwala-gwalai da dukiya, domin rayuwar karkashin kasa, wato underworld.

Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri
Tarihin yadda kasar Misra ta samu Dalar tsandauri

Talasimai, layu, da rubuce rubuce ke kewaye da gawarwakin, wadanda a fatansu, tsafin da zai tayar da su kenan bayan mutuwarsu.

Wasu fir'aunoni an taras dasu da bayinsu da mata da aka binne da ransu, saboda su taya su hidima a waccan sabuwar rayuwa da suke sa rai zasu yi.

Barayin kaburbura dai sukan zo su washe wadannan kaburbura, duk da tsinuwa da tsafi da dabaru na boye kaburburan a lokuna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng