Mamdani Ya Fadi Me Doka Ta Ce kan Batun Cafke Netanyahu a Amurka
- Magajin garin birnin New York, Zohran Mamdani, ya amince cewa ba shi da ikon doka na kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu
- Mamdani ya ce gwamnatin tarayya ce kawai ke da hurumin aiwatar da sammacin kamu da Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya (ICC) ta fitar
- Furucin magajin garin ya zo ne bayan ya sha bayyana cewa zai yi kokarin kama Benjamin Netanyahu idan ya ziyarci birnin New York a Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
New York, Amurka – Magajin garin birnin New York, Zohran Mamdani, ya bayyana cewa ba shi da ikon doka da zai ba shi damar kama Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, idan ya ziyarci birnin.
Mamdani ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo, inda ya ce gwamnatinsa ta binciki duk hanyoyin doka domin tantance ko za su iya aiwatar da sammacin kama Netanyahu.

Kara karanta wannan
Da gaske gwamnatin Tinubu ta karbo bashin Naira tiriliyan 80? Minista ya yi martani

Source: Getty Images
CNN ta rahoto cewa magajin garin ya ce binciken ya nuna a sarari cewa gwamnatin birnin New York ba ta da ikon aiwatar da irin wannan sammaci.
Abin da Mamdani ya ce
A cikin bidiyon da Zohran Mamdani ya wallafa a shafinsa na X ya ce an yi cikakken bincke domin ganin ko zai iya kama Netanyahu bisa doka.
Ya ce:
"Gwamnatina ta binciki duk hanyoyin da doka ta tanada domin gano ko birnin New York zai iya aiwatar da sammacin kamu da ICC ta fitar idan Benjamin Netanyahu ya zo nan."
"Ya bayyana a fili cewa ba mu da ikon doka mai zaman kanta na aiwatar da wannan sammaci. Amma gwamnatin tarayya tana da wannan iko, kuma ina kira gare ta da ta aiwatar da sammacin."
Kalaman nasa sun bambanta da waɗanda ya yi kwanaki kaɗan da suka gabata a wata hira, inda ya ce yana aiki tare da lauyoyin gwamnatinsa kan hanyoyin kama Netanyahu saboda zargin aikata laifuffukan yaƙi.
Trump ya kare Netanyahu
Wani rahoton ya nuna cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya shiga cikin muhawarar kama Netanyahu a ranar Litinin ta hanyar wani saƙo da ya fitar.

Source: Getty Images
Trump ya ce Netanyahu ba zai fuskanci kamu ba muddin yana cikin Amurka.
Ya sanar da cewa:
"Ba za a kama Benjamin Netanyahu ba ta kowace hanya ko a kowane yanayi yayin da yake cikin Amurka."
Ana sa ran Netanyahu zai halarci taron Babban Zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) da za a gudanar a New York daga baya a wannan shekarar.
Ga abin da Mamdani ya fada a bidiyo:
Trump ya yi yarjejeniya da Saudi
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Amurka Donald Trump ya amince da wata yarjejeniya da Saudiyya kan shirin makamashin nukiliya na farar hula.
Rahotanni sun ce yarjejeniyar za ta ba Saudiyya damar haɓaka sinadarin uranium domin amfani da shi a shirin nukiliyar ƙasar tare da haɗin gwiwar kamfanonin Amurka.
Ana sa ran yarjejeniyar za ta kasance na tsawon shekaru 30, kuma za a sanar da ita a hukumance nan ba da jimawa ba kasancewar ba a yi cikakken bayani ba.
Asali: Legit.ng
