An Fitar da Hotunan Sojojin Amurka da Iran Ta Kashe a Jordan

An Fitar da Hotunan Sojojin Amurka da Iran Ta Kashe a Jordan

  • Ma'aikatar yakin Amurka ta bayyana sunayen sojoji biyu da suka mutu a hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kai kan sansaninta a Jordan
  • Sojojin da suka mutu sun haɗa da Tyler James Feehan mai shekaru 25 daga Hawaii da Isabella Gonzales mai shekaru 19 daga Texas
  • Pentagon ta ce kusan sojojin Amurka 100 sun jikkata tun bayan fara rikicin, yayin da ake ci gaba da binciken gawar wani da aka gano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington DC – Ma'aikatar Yakin Amurka (Pentagon) ta bayyana sunayen sojoji biyu da suka mutu sakamakon hare-haren da Iran ta kai kan sansanonin sojojin Amurka da ke ƙasar Jordan.

Pentagon ta ce sojojin da suka rasa rayukansu su ne Tyler James Feehan mai shekaru 25 daga jihar Hawaii da Isabella Gonzales mai shekaru 19 daga jihar Texas.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An kai wa Fulani hari suna tsakiyar kiwo a Filato, an rasa rayuka

Tyler James Feehan da Isabella Gonzales
Tyler James Feehan da Isabella Gonzales da Iran ta kashe a Jordan. Hoto: US Army
Source: Facebook

Rahoton NBC ya nuna cewa Gonzales ta mutu ne a ranar Juma'a, yayin da Feehan ya rasu a ranar Asabar, sai dai Pentagon ba ta bayyana cikakken yanayin da ya jawo mutuwarsu ba.

Waɗanne ayyuka sojojin ke yi?

Ma'aikatar yakin ta bayyana cewa Feehan yana aiki ne a rundunar kariya daga makamai masu linzami da ke Fort Bragg a North Carolina.

Ita kuwa Gonzales tana aiki ne a rundunar kariya daga makamai masu linzami da ke Ansbach a ƙasar Jamus.

Pentagon ta ce dukkansu suna cikin Operation Inherent Resolve, wani shiri da Amurka ta fara tun shekarar 2014 domin yaƙi da ƙungiyar ISIS.

Sai dai ta jaddada cewa ba sa cikin aikin yaƙin da Amurka ke yi da Iran wanda ake kira Operation Epic Fury.

Duk da bayanin Pentagon, Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sojojin sun mutu ne yayin da suke aiki domin hana Iran mallakar makamin nukiliya.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Abin da Trump ya ce bayan Iran ta kashe sojojin Amurka

A wani lamari dabam, Legit Hausa ta rahoto cewa Pentagon ta kuma tabbatar da mutuwar wani sojan Amurka a ƙasar Iraki.

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka na yi wa jama'a bayani. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Ana binciken wasu gawarwaki

Rundunar Amurka ta CENTCOM ta sanar cewa ta gano wasu gawarwakin da ba a tantance ko su wanene ba yayin binciken da ake yi kan wani sojan Amurka da ya ɓace bayan harin Iran a Jordan.

Jami'an rundunar sun ce ana gudanar da binciken ƙwayoyin halitta domin tabbatar da ko gawarwakin na wannan sojan da ake nema ne.

Rahoton da AP ta fitar ya nuna cewa Pentagon ta bayyana cewa kusan sojojin Amurka 100 sun jikkata tun bayan fara hare-haren baya-bayan nan.

Trump ya nuna alhininsa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana mutuwar sojojin Amurka a Jordan a matsayin abin takaici matuƙa.

Trump ya ce sojojin sun mutu ne suna hidimar ƙasarsu, yana mai jaddada cewa Amurka ba za ta bari Iran ta mallaki makamin nukiliya ba.

Bayan harin da Iran ta kai kan sansanonin Amurka a Jordan, rundunar sojin Amurka ta mayar da martani ta hanyar kai hare-haren sama kan wasu wuraren da take zargin na Iran ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng