Abubuwan Sun Ƙara Zafi, Kasar Musulunci Ta Iran Ta Sake Yi Wa Amurka Babbar Illa

Abubuwan Sun Ƙara Zafi, Kasar Musulunci Ta Iran Ta Sake Yi Wa Amurka Babbar Illa

  • Dakarun kare juyin juya halin na kasa Iran sun bayyana cewa sun samu nasarar harbo jirgin MQ-9 Reaper na Amurka a birninnAhvaz
  • Kasar Iran ta ce wannan shi ne jirgin MQ-9 na hudu da ta harbo cikin kwanaki takwas da suka gabata
  • Mahukuntan Iran sun yi ikirarin cewa sun lalata sama da jiragen Amurka 150 tun bayan fara yakinn kasar da kasashen Amurka da Isra'ila

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Dakarun Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran (IRGC) sun sanar da cewa sun harbo wani jirgin leken asiri da kai hari na MQ-9 Reaper mallakin Amurka a sararin samaniyar birnin Ahvaz.

A cewar mahukuntan Iran, wannan shi ne jirgin MQ-9 na hudu da suka harbo cikin kwanaki takwas da suka gabata, bayan sake barkewar yaki tsakanin kasashen biyu.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali: Girgizar kasa mai girma ta afku a Jamhuriyar Musulunci ta Iran

Jirgin Amurka.
Jirgin leken asiri da kai hari na kasar Amuka Hoto: Miguel J. Rodriguez
Source: Getty Images

Iran ta lalata jiragen Amurka sama da 150

Rahoton tashar Al-Jazeera ya nuna cewa mahukuntan Iran sun kuma yi ikirarin cewa sun harbo sama da jiragen Amurka 150 tun bayan barkewar yakin.

A cewarsu, kusan jirage 30 daga cikin wadanda aka lalata nau'in MQ-9 Reaper ne, wanda ake amfani da shi wajen leken asiri da kai hare-hare.

Wannan n zuwa ne yayin da yaki ya sake barkewa tsakanin Amurka da kasar Musulunci ta Iran, lamarin da ke kara zama barazana ga tattalin arzikin duniya.

Iran ta kalubalanci ikirarin Amurka

A makon farko na watan Maris, Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya bayyana cewa kasarsa na da cikakken iko kan sararin samaniyar Iran.

Sai dai Iran ta ce sababbin da kuma ingantattun tsarin kariyar sararin samaniyarta sun nuna akasin wannan ikirari., tana ami cewa yanzu ita ke da cikakken iko.

A cewar ksar ta Musulunci, idan har da gaske ta lalata jiragen MQ-9 guda 30, hakan na nuna cewa ikirarin gwamnatin Amurka ba daidai ba ne.

Kara karanta wannan

Yaki ya yi zafi: Amurka ta kai sababbin hare hare kan Iran bayan kashe sojojinta

Asarar da za ta iya kai wa biliyoyin daloli

Rahotanni sun nuna cewa matsakaicin kudin kera jirgin leken asiri na MQ-9 Reaper ya kai kusan Dala miliyan 34 a shekarar 2024.

Iran da Amurka.
Jagoran addinin kasar Iran, Mojtaba Khamenei da shugaban Amurka, Donald Trump Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Idan har ikirarin Iran na lalata jiragen guda 30 cikin watanni hudu gaskiya ne, hakan na nufin Amurka ta yi asarar kayan aikin soja da darajarsu ta haura Dala biliyan daya.

Kasashen dai na ci gaba da kai wa juna hare-hare tun bayan karya yarjejeniyar tsagaita wuta da suka cimma wa kwanakin baya, wanda hakan ya zama barazana ga tattaunawar da aka fara.

Iran ta hallaka sojojin Amurka 2

A wani rahoton, kun ji cewa Iran ta kashe sojojin Amurka biyu a Jordan bayan ta kai wani harin makamai masu linzami kan sansanin da suke ciki a Gabas ta Tsakiya.

An kashe sojojin ne yayin da suke kare kansu daga hare-haren makamai masu linzami masu cin dogon zango da jirage marasa matuƙa da Iran ta kai, a ranar Juma’a, 17 ga Yuli, 2026.

Wannan ne karon farko da aka kashe sojojin Amurka tun bayan da aka sake komawa faɗa makonni biyu da suka gabata. Lamarin ya sa adadin sojojin Amurka da aka kashe a yaƙin ya kai 16.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262