Shugaban Kasa Ya Haramta Zabe Kwata Kwata, zai Cigaba da Mulki a Nicaragua
- Shugaban ƙasar Nicaragua, Daniel Ortega ya bayyana cewa ƙasarsa ba za ta ƙara gudanar da zaɓen shugaban kasa ba
- A bayanin da ya yi, Ortega ya ce matakin na da nufin hanawa 'yan adawa damar ƙoƙarin ƙwace iko da komawa kan mulki
- Masana da 'yan adawa sun bayyana cewa matakin yana nuna tsoron da shugaban da matarsa ke ji na shan kaye a zabe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Managua – Shugaban ƙasar Nicaragua da ya daɗe a kan mulki, Daniel Ortega, ya bayyana cewa ƙasar ba za ta sake gudanar da zaɓe ba, matakin da ya rufe duk wata dama ta ƙalubalantar mulkinsa idan wa'adinsa ya ƙare a shekara mai zuwa.
Ortega, wanda ke riƙe da mulki tun shekara ta 2007 bayan farkon mulkinsa a shekarun 1980, ya ce wannan mataki zai dakatar da duk wata hanya da 'yan adawa za su bi don karɓar mulki, ko da yake bai yi bayani kan yadda za a aiwatar da haramcin ba.

Source: Getty Images
CNN ta ruwaito cewa Ortega ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a lokacin wani jawabi na tunawa da juyin juya halin Sandinista na shekarar 1979, inda ya taimaka wajen kifar da mulkin kama-karyar Anastasio Somoza wanda Amurka ke goyon baya.
Abubuwan da Ortega ya bayyana
Mataki yana zuwa ne yayin da gwamnatin Amurka ta bayyana gwamnatin Ortega a matsayin ta kama-karya, sannan ta sanya wa jami'an ƙasar fiye da 2,350 da 'yan uuwansu takunkumi.
A cikin jawabinsa na farko tsawon watanni biyu, tsohon shugaban mai shekaru 80 ya aike da saƙon gargadi ga makiyansa.
Reuters ta rahoto cewa ya ce:
"Ba za a sake yin wani zaɓe a nan ba domin su yi ƙoƙarin ƙwace gwamnati da karɓar iko. Ranakun da jam'iyyu masu goyon bayan Amurka da 'yan Somocistas za su koma kan mulki sun ƙare - ba za su sake komawa ba."
Martanin masana da 'yan adawa

Kara karanta wannan
A karshe, Peter Obi ya bar boye boye, ya fadi dalilin daukar Kwankwaso mataimakinsa
Masana siyasa da 'yan adawa dake gudun hijira sun bayyana cewa wannan furuci na nuna ainihin yanayin mulkin Ortega da matarsa, sannan ya fallasa tsoron da suke ji.
Felix Maradiaga, wanda ya kasance 'dan takarar shugaban ƙasa na 'yan adawa da aka ɗaure daga 2021 zuwa 2023 kafin a fitar da shi zuwa Amurka, ya bayyana cewa kalaman da Ortega ya yi ba nuna ƙarfi ba ne, illa tsoro na zahiri.

Source: Getty Images
Tiziano Breda, babban mai bincike a cibiyar ACLED, ya bayyana cewa Ortega da matarsa sun zaɓi soke gudanar da zaɓe baki ɗaya saboda fargabar da suke ji na bayyanar adawa da za ta iya girgiza mulkinsu.
Faransa ta gargadi Iran
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin Emmanuel Macron ta kasar Faransa ta gargadi Iran da cewa ta ci zarafin wasu jami'anta.
Ofishin ma'aikatar harkonkin wajen Faransa ya yi zargin cewa an kama jami'an biyu an masu tambayoyi, amma daga bayan an sake su.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da takun saka a Gabas ta Tsakiya, inda Iran da Amurka ke cigaba da kai wa juna hare-hare.
Asali: Legit.ng
