Sojojin Ukraine Sun Cafke 'Dan Najeriya da Ya Shigarwa Rasha Yaki

Sojojin Ukraine Sun Cafke 'Dan Najeriya da Ya Shigarwa Rasha Yaki

  • Sojojin Ukraine sun cafke wani matashi ɗan Najeriya da ke yaƙi a bangaren sojojin Rasha a yankin Zaporizhzhia
  • An bayyana cewa ya shiga rundunar Rasha ne domin rage masa hukuncin gidan yari bayan an kama shi da laifin miyagun ƙwayoyi
  • Rahotanni da suka fito sun sun ce Rasha ta ɗauki dubban 'yan ƙasashen waje domin tura su zuwa fagen yaƙi a Ukraine

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Ukraine – Rundunar yaki da ke goyon bayan Ukraine, ta cafke wani ɗan Najeriya mai suna Kehinde Oluwagbemileke da ke yaƙi tare da sojojin Rasha a yankin Zaporizhzhia.

Wata majiya a Ukraine ta tabbatar da cewa an kama Oluwagbemileke mai shekaru 29 a yayin da yake cikin rundunar Rasha da ya shafe watanni biyar yana yaƙi da Ukraine.

Kehinde Oluwagbemileke da aka kama a Ukraine
Kehinde Oluwagbemileke da aka kama a yakin Ukraine. Hoto: @iamayims
Asali: Twitter

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa ɗan Najeriyan ya zauna a Rasha tsawon shekara huɗu kafin daga bisani aka kama shi da laifin da ya shafi miyagun ƙwayoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'dan Najeriya ya zama sojan Rasha

Bayan kama shi da laifin ne ya sa aka ba shi zaɓi tsakanin zaman gidan yari ko shiga rundunar soja.

Rahoton hukumar Ukraine ya ce:

“Kehinde ɗaya ne daga cikin dubban dakarun haya daga ƙasashen ketare da Ma’aikatar Tsaron Rasha ke ɗauka don tura su zuwa Ukraine.”

An bayyana cewa an kama shi bisa laifin da ya shafi miyagun ƙwayoyi a ƙarƙashin Sashe na 228 na Dokar Laifuka ta Rasha.

Vanguard ta wallafa cewa shi da kan shi ya zaɓi shiga rundunar soji don rage hukuncin zaman gidan yari da zai fuskanta.

Dubban 'yan ƙetare na cikin rundunar Rasha

Rasha na ci gaba da ɗaukar mutane daga ƙasashen Afirka da Asiya don shiga rundunarta, musamman ma waɗanda ke fuskantar hukunci a gidajen yari ko matsin tattalin arziki.

Wata kungiyar mai suna “I Want to Live” ta ce:

“Mun riga mun wallafa bayanan kusan dakarun haya 7,000 daga ƙasashe 14 da ke fagen fama a Ukraine,”

Kungiyar ta yi zargin ana samun ‘yan haya daga ƙasashen waje da araha da ake watsi da su cikin sauƙi ba tare da kulawa ba, kuma hakan ya ƙara tayar da hankalin masu kare hakkin ɗan adam.

A makon da ya gabata ma, sojojin Ukraine sun kama wani ɗan ƙasar China, Wang Wu, ɗan shekara 24, wanda shi ma ke yaƙi a gefen sojojin Rasha.

An zargi Rasha da rashin kula da sojojin haya
An zargi Rasha da rashin kula da sojojin haya. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Har yanzu hukumomin Najeriya ba su ce komai ba kan kama ɗan ƙasar da ke cikin rundunar Rasha, duk da irin damuwar da hakan ke haifarwa.

An kama 'dan Najeriya da ya damfari Amurka

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar binciken Amurka ta FBI ta kama wani dan Najeriya da ake zargi ya yi damfara a kasar.

Rahoto ya nuna cewa matashi dan Najeriyan ya bude asusun bogi kuma ta nan aka tura masa makudan kudi a bikin rantsar da Donald Trump.

Hukumomin kasar Amurka sun bi diddigin matashin kuma daga baya sun gano cewa yana zaune ne a jihar Legas da ke Kudancin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng