Kasashen Afrika Sun Zabi Shugaban Kasa Mai Shekaru 46 a matsayin Shugaban ECOWAS
- Ba da dadewa ba aka zabi Shugaban kasar Sanegal, Bassirou Diomaye Faye, a matsayin sabon kungiyar ECOWAS
- An gudanar da zaben ne yayin taron ECOWAS na musamman karo na 69 da aka yi a kasar Sierra Leone ranar Lahadi
- Faye ya karbi mulki daga hannun Julius Maada Bio, zai jagoranci Hukumar Shugabannin Kasashe da Gwamnatoci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Sierra Leone - Diomaye Bassirou Faye, aka zaba a matsayin sabon shugaban kungiyar da ke kula da kasashen Afrika ta yamma.
Shugaban kasar Sanagal zai rike kungiyar ECOWAS da aka kafa a shekarar 1975 domin cigaban kasashen yammacin Afrika.

Source: Getty Images
A daren Lahadi, 19 ga watan 2026, tashar Channels ta rahoto cewa Diomaye Bassirou Faye ya samu shugabancin kungiyar ECOWAS.
An cin ma wannan matsaya ne bayan wani taro na 69 da kungiyar ta yi a kasar Sierra Leone kamar yadda kungiyar ta sanar a shafin yanar gizo.

Kara karanta wannan
Tura ta kai bango: Mutanen gari sun aika sako ga Tinubu kan hare haren 'yan bindiga
Diomaye Faye zai canji Maada Bio a ECOWAS
Julius Maada Bio zai mika ragamar shugabantar kungiyar zuwa ga takawaransa na kasar Sanagal mai shekaru 46 da haihuwa.
Shugaba Julius Maada Bio na kasar Sierra Leone zai bar ofis ne bayan ya yi shekara guda yana rike da wannan babban mukami.
Maada Bio ya gaji Bola Ahmed Tinubu na Najeriya ne lokacin da wa’adinsa a kungiyar ECOWAS ya zo karshe a Yunin 2025.
Shi Tinubu ya rike kujerar sau biyu bayan nada shi da aka yi jim kadan da zama sabon shugaban Najeriya a tsakiyar 2023.
Faye zai ci karo da matsaloli a ECOWAS
Rahoton ya ce shugaba Faye zai shiga ofis lokacin da kungiyar ECOWAS ta ke fuskantar barazanar tsaro da matsaloli na cikin gida.
Tuni kasashen Mali, Burkina Faso da Jamhuriyyar Nijar suka barke daga kungiyar bayan sojojin sun kifar da gwamnatocin farar hula.
Sanarwar nadin Faye ya fito ne daga kakakin Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya, Kimiebi Imomotimi Ebienfa a birnin tarayya Abuja.

Source: Getty Images
Leadership ba ta kawo wani karin bayani dangane da sanarwar Kimiebi Imomotimi Ebienfa ba.
Masu sharhi a kan harkokin yau da gobe sun ce Faye yana cikin sababbin jinin shugabanni da ake da su yanzu a kasashen Afrika.
Wannan kujera ta kara masa nauyi a kan wadanda suke wuyansa kuma za ta iya yi wa Sanagal tasiri zuwa lokacin da zai bar ofis.
Yanzu haka akwai matsalolin siyasa a Sanagal har ta kai shugaba Faye ya rushe gwamnatin kasar sakamakon rigimarsa da Ousmane Sanko.
Bayan korarsa ne Sanko ya zama shugaban majalisa a Sanagal. Wasu na ganin yana harin kujerar shugaban kasa a zaben 2029.
Bola Tinubu ya bar kujerar ECOWAS
Labari ya zo cewa wa'adin Shugaba Bola Tinubu na jagorantar ƙungiyar ECOWAS ya zo ƙarshe (a ranar Lahadi, 7 ga watan Yulin 2024.
Alokacin an ji cewa ana sa ran shugabannin ƙungiyar za su zaɓi sabon shugaba a babban taron ƙungiyar karo na 65 da aka yi a Abuja.

Kara karanta wannan
Gwamnoni 6 sun shirya zuwa wurin Bola Tinubu kan tikitin musulmi da musulmi a zaben 2027
Akwai matsalolin da Tinubu ya fuskanta lokacin mulkinsa, musamman juyin mulkin soji da aka yi a wasu ƙasashe uku na yammacin Afrika.
Asali: Legit.ng
