Toh fah: Ana yunkurin hana 'yan Najeriya shiga Amurka

Toh fah: Ana yunkurin hana 'yan Najeriya shiga Amurka

- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump kokarin kara yawan kasashen da Amurka za ta hana ‘yan kasar shiga cikinta

- Kasashen dai wadanda suka kasance guda hudu duk daga yankin Afirka sun hada da; Najeriya, Tanzania, Sudan da Eritrea

- Koda dai ba a bayyana kasashen ba, ana sanya ran cewa a mako mai kamawa ne za a saki jerin sunayen kasashen wadanda za a hana su bizar Amurka

Rahotanni sun nuna cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump na kan yin wani yunkuri na kara yawan kasashen da Amurka za ta hana ‘yan kasar shiga cikinta.

Kasashen dai wadanda suka kasance guda hudu duk daga yankin Afirka sun hada da; Najeriya, Tanzania, Sudan da Eritrea.

Trump wanda ya bayyana hakan a wata hira da mujallar Wall Streer Journal a lokacin taron koli kan tattalin arziki na duniya a Davos, Switzerland, ya tabbatar da cewa yana kokarin fadada jerin sunayen kasashen da za a hana shiga Amurka amma bai fadi sunayensu ba.

A mako mai kamawa ne dai ake sa ran za a saki jerin sunayen kasashen wadanda za a hana su bizar Amurka.

KU KARANTA KUMA: Rundunar soji ta yi gargadi kan tashohin bincike na bogi a titin Maiduguri-Damaturu

A watan Satumbar 2017 ne dai shugaba Trump ya sanya takunkumin hana bizar shiga Amurka ga kasashen Iran da Libya, Somalia, Syria da kuma Yemen.

A 2018 ne kuma kotun kolin kasar ta amince da hukuncin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel