Ghana: Matar Tsohon Shugaban Kasa Ta Riga Mu Gidan Gaskiya Tana da Shekaru 79

Ghana: Matar Tsohon Shugaban Kasa Ta Riga Mu Gidan Gaskiya Tana da Shekaru 79

  • Kasar Ghana ta yi babban rashin bayan sanar da rasuwar matar tsohon shugaban kasar kuma mai kare haƙƙin mata
  • An tabbatar da cewa Nana Konadu Agyeman-Rawlings, ta rasu tana da shekaru 76 bayan gajeriyar rashin lafiya
  • Marigayiyar matar Jerry John Rawlings, ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da dokokin da suka kare haƙƙin mata da yara a ƙasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Accra, Ghana - Kasar Ghana ta shiga jimami bayan sanar da rasuwar matar tsohon shugabanta bayan fama da jinya.

Marigayiyar wacce kafin rasuwarta mai fafutukar kare haƙƙin mata ce, Nana Konadu Agyeman-Rawlings, ta rasu tana da shekara 76 a duniya.

Matar tsohon shugaban kasar Ghana ta rasu
Matar tsohon shugaban kasar Ghana kenan a taro kafin rasuwarta. Hoto: @MrRockson.
Source: Twitter

Rahoton BBC ya ce ita ce matar tsohon shugaban ƙasar Ghana, Jerry John Rawlings, wanda ya rasu shekaru biyar da suka gabata bayan ya yi mulki na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Magana ta kare, Tinubu ya rantsar da sabon shugaban hukumar zaben Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rawlings ya jagoranci juyin mulki biyu a kasar Ghana kafin daga bisani a zaɓe shi sau biyu a matsayin shugaban ƙasa a tsarin jam’iyyu da dama.

Yaushe marigayiya Agyeman-Rawlings ta rasu?

Rahotanni sun bayyana cewa Agyeman-Rawlings ta rasu da safiyar Alhamis 23 ga watan Oktobar 2025 bayan gajeriyar rashin lafiya, a cewar mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa, Felix Kwakye Ofosu.

Iyalan marigayiyar sun sanar da shugaban ƙasa, John Dramani Mahama rasuwarta da yammacin yau Alhamis.

Shugaba Mahama, wanda ke jagorantar jam’iyyar NDC da Rawlings ya kafa, ya yi shiru na girmamawa yayin rantsar da sababbin alkalan kotun koli.

An sanar da rasuwar matar tsohon shugaban kasar Ghana
Shugaban kasar Ghana yayin taro a Accra. Hoto: Ernest Ankomah.
Source: Getty Images

Takaitaccen tarihin marigayiya Agyeman-Rawlings

An haifi Nana Konadu a watan Nuwamba 1948 a Cape Coast, kuma ta fito daga iyali mai matsakaicin hali a Ghana.

Ta halarci makarantar Achimota a Accra, inda ta hadu da mijinta Jerry Rawlings, kafin daga baya ta yi karatun zane da yadudduka.

Kara karanta wannan

ASUU ta janye yajin aiki a jami'o'i, ta kafa wa gwamnatin Tinubu sharadi

Sun haifi ’ya’ya hudu ciki har da Dr. Zanetor Agyeman-Rawlings, ’yar majalisa a jam’iyyar NDC a yau, kamar yadda Africanews ta ruwaito.

Agyeman-Rawlings ta taka muhimmiyar rawa wajen tsara manufofin gwamnati da suka taimaka wajen kare haƙƙin mata a Ghana.

Ta taimaka wajen kafa dokar 1989 da ta tabbatar da gadon mata da yara, da kuma sashen da ya tabbatar da daidaito a kundin tsarin mulki na 1992.

Agyeman-Rawlings kanta ta shiga siyasa, inda ta nemi takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NDC a 2012, amma ba ta samu nasara ba.

Ƙungiyarta ta mayar da hankali wajen ƙarfafa mata da raya al’umma ta hanyar sana’o’i da ilimi da sauran bangarori na rayuwa.

Ghana: Ministoci sun mutu a hatsarin jirgin sama

Kun ji cewa an samu mummunan hatsarin jirgin sama a yankin Ashanti da ke kasar Ghana mai makwabtaka da Najeriya a ranar Laraba 6 ga watan Agustan 2025.

Ministan tsaro da na muhalli a ƙasar Ghana sun mutu tare da wasu mutum shida a hatsarin wanda ya daga hankulan jama'a.

Sojojin Ghana sun ce jirgin Z9 na daga Accra zuwa Obuasi ya bace daga sama, inda yake dauke da mutane takwas ciki har da mukarraban gwamnati.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.