Ana tsakiyar Musayar Wuta, Iran Ta Samu Gagarumin Goyon Baya a Yaki da Amurka

Ana tsakiyar Musayar Wuta, Iran Ta Samu Gagarumin Goyon Baya a Yaki da Amurka

  • Firayim Minista Anwar Ibrahim ya yaba wa Pakistan kan yunkurin shiga tsakanin Amurka da Iran domin kawo karshen yakin Gabas ta Tsakiya
  • Malaysia ta jaddada cewa Iran tana da hakkin kare kanta karkashin dokokin kasa da kasa yayin da Isra'ila ke kai mata hare-hare ba kakkautawa
  • Anwar ya yi kira ga manyan kasashen duniya da su daina nuna son zuciya wajen amfani da dokokin duniya ta hanyar goyon bayan bangare daya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Malaysia - Firayim Ministan ƙasar Malaysia, Anwar Ibrahim, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga tayin da Pakistan ta yi na karɓar bakuncin tattaunawar sulhu tsakanin Amurka da Iran.

Anwar ya bayyana wannan yunƙuri a matsayin wanda ya zo a daidai gaba, duba da yadda takaddama ke ƙara ƙaruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Pakistan za ta shiga tsakani a yakin Amurka da Isra'ila ke gwabzawa da Iran

Malaysia ta goyi bayan Iran ta kare kanta daga hare-haren Amurka da Isra'ila
Hagu zuwa dama: Firayim Ministan Malaysia, Anwar Ibrahim; Ministan wajen Iran, Abbas Araghchi da Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: @anwaribrahim/X, Anna Moneymaker / ATTA KENARE via Getty Images
Source: Getty Images

Malaysia na tare da Iran a yakin Amurka

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, 25 ga Maris, 2026, Anwar Ibrahim ya yaba wa takwaransa na Pakistan, Shehbaz Sharif, kan yadda ya nuna jajircewa wajen buɗe ƙofar diflomasiyya a wannan mawuyacin lokaci.

Ya bayyana cewa:

“Matsayin Pakistan a duniyar Musulmi da kuma dangantakarta da ɓangarorin da abin ya shafa, ya ba ta damar samar da yanayi mai kyau na tattaunawa.”

Baya ga goyon bayan sulhun, Malaysia ta sake jaddada matsayinta na goya wa Iran baya na kare kanta daga hare-haren Amurka da Isra'ila.

Anwar ya bayyana cewa:

“Malaysia ta tabbatar da haƙƙin Iran na kare ikon ƙasarta, kamar yadda dokokin ƙasa da ƙasa suka amince da shi, musamman duba da hare-haren Isra'ila da ake ci gaba da kai wa a ƙasar da kuma Lebanon.”

Malaysia ta aika sako ga Iran da Amurka

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Iran ta yi martani kan ikirarin Trump na fara tattaunawa kan yakin da ake yi

Duk da haka, Firayim Ministan ya yi kira ga dukkan ɓangarorin da su nuna matuƙar kamun kai domin tabbatar da cewa ba a jawo farar hula da sauran ƙasashen yankin, musamman ƙasashen Gulf, cikin wannan rikici ba.

Ya jaddada cewa tattalin arziki da zaman lafiyar duniya suna fuskantar babban haɗari idan har aka bar yaƙin ya faɗaɗa fiye da yadda yake yanzu.

Anwar Ibrahim ya soki yadda wasu ƙasashe ke amfani da dokokin ƙasa da ƙasa ta hanyar son zuciya. A cewarsa, yarda da tsarin dokokin duniya ya dogara ne kan yin adalci ga kowa ba tare da nuna bambanci ba.

Firayim Ministan Malaysia, Anwar Ibrahim ya aika sako ga kasashen Amurka, Iran da Isra'ila.
Firayim Ministan Malaysia, Anwar Ibrahim ya na jawabi a gaban rundunar 'yan sandan kasarsa, PDRM. Hoto: @anwaribrahim
Source: Twitter

Kokarin Pakistan a yakin Gabas ta Tsakiya

A game da hakan, Anwar Ibrahim ya ce:

“Dokokin ƙasa da ƙasa ba za su iya zama garkuwa ga ɓangare ɗaya da yaki bin doka ba, yayin da ake hana ɗayan bangaren haƙƙinsa na kare kansa.”

A kwanakin nan, Anwar ya bayyana cewa ya tattauna da shugabannin ƙasashen Turkiyya, Masar, Indonesia, Japan da Pakistan domin neman hanyoyin kwantar da tarzoma.

Malaysia ta sha alwashin cewa za ta ci gaba da mara baya ga duk wani yunkuri na gaskiya, wanda zai kai ga samar da adalci da zaman lafiya mai dorewa a duniya.

Kara karanta wannan

Lamari ya kwabe: Saudiyya ta kori sojoji, jami'an diflomasiyyar Iran daga kasar

Karanta sanarwar a nan kasa:

Iran ta ci gaba da kai hare-hare Isra'ila

A wani labari, mun ruwaito cewa, Rundunar dakarun IRGC ta Iran ta sanar da kaddamar da rukuni na 80 na hare-haren ramuwar gayya mai suna "Operation True Promise 4".

A wannan karon rundunar ta kai hari kan wasu muhimman wurare da cibiyoyin sojoji a yankin Arewacin Isra'ila, baya ga luguden wuta kan sansanonin Amurka da ke fadin yankin.

Ta ce an kaddamar da harin ne domin nuna goyon baya ga "hare-hare na alfahari" da kungiyar gwagwarmayar Hezbollah ta Lebanon ke kaiwa kan Isra'ila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com