Martanin Trump kan Mutuwar Sanatan Amurka da Ke Zuga Shi kan Yaki da Iran
- Donald Trump ya yi alhinin rasuwar Sanatan jam'iyyar Republican, Lindsey Graham, yana mai cewa yana cikin fitattun sanatocin da ya taɓa sani
- Ofishin Graham ya sanar cewa ya rasu ne da yammacin Asabar bayan gajeriyar rashin lafiya mai zuwa ba-zata, yana da shekara 71
- Shugabannin siyasa daga Amurka da Isra'ila sun bayyana alhini tare da yabawa gudunmawar Graham a siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Washington, DC - Shugaban Amurka Donald Trump ya yi martani kan rasuwar fitaccen sanatan jam'iyyar Republican, Lindsey Graham, wanda ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.
Shugaba Trump ya bayyana cewa Sanata Lindsey Graham yana daya daga cikin manyan sanatocin da ya taba sani.

Source: Getty Images
Shugaban kasar na Amurka ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Lahadi, 12 ga watan Yulin 2026.
Daraktan sadarwa na ofishin Graham ya sanar a wani sako da aka wallafa a shafin X da safiyar Lahadi cewa sanatan ya rasu ne da yammacin ranar Asabar, 11 ga watan Yulin 2026.
Sanata Lindsey Graham ya rasu yana da shekara 71, yayin da iyalansa suka bukaci a mutunta sirrinsu a wannan lokaci na jimami.
Trump ya yabi Lindsey Graham
Trump ya bayyana Graham a matsayin ɗaya daga cikin manyan mutane da sanatocin da ya taɓa sani.
A cikin saƙonsa, Trump ya ce:
"Sanata Lindsey Graham, ɗaya daga cikin mafiya nagartar mutane da sanatocin da na taɓa sani, ya rasu! Ya kasance mutum mai aiki tuƙuru kuma ɗan kishin ƙasar Amurka na gaske. Za a yi matuƙar kewarsa. Za a sanar da cikakkun bayanai da shirye-shiryen jana'iza nan gaba. Abin takaici ƙwarai."
Tarihin Lindsey Graham
An zaɓi Graham a Majalisar Dattawan Amurka a shekara ta 2002, sannan aka sake zaɓensa a shekarun 2008, 2014 da 2020.
Kafin hakan, ya wakilci mazaba ta uku ta jihar South Carolina a Majalisar Wakilan Amurka daga shekarar 1995 bayan an zaɓe shi a 1994.
A fagen manufofin ƙasashen waje, Graham ya kasance mai goyon bayan mamayar Iraki da Amurka ta yi a 2003. Haka kuma ya dade yana kira da a ɗauki matakin soja kan Iran.
Ya kasance mai goyon bayan Isra'ila, kuma ya kasance ɗaya daga cikin manyan abokan hulɗar Trump a Majalisar Dattawa bayan sun sasanta duk da cewa Graham ya soki Trump lokacin neman tikitin takarar shugaban ƙasa na Republican a 2016 kafin daga bisani ya janye daga takarar.
Shugabanni sun yi alhinin rasuwar Graham
Shugaban Isra'ila, Isaac Herzog, ya ce labarin rasuwar Graham ya girgiza shi kuma ya sanya shi matuƙar takaici, kamar yadda ya sanya a shafinsa na X.
A cewarsa:
"Sanata Graham ya kasance fitila ta gaskiya da kuma jagora na haɗin gwiwar Amurka da Isra'ila."
Ya ƙara da cewa al'ummar Isra'ila ba za su manta da yadda Graham ya tsaya masu a lokutan ƙalubale ba, kuma za su ci gaba da gode masa saboda adalci, gaskiya da aminci da ya nuna.

Source: Twitter
Shi ma gwamnan jihar South Carolina, Henry McMaster, ya bayyana Graham a matsayin mutum da ba za a iya maye gurbinsa ba.
McMaster ya ce:
"Shi ne jajirtaccen mai fafutukar kare muradun South Carolina da Amurka, kuma aboki ne mai aminci da riƙon amana."
Wasiyyar da Trump ya bari kan Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ya riga ya bayar da umarni kan abin da za a yi idan Iran ta yi nasarar raba shi da duniya.
Shugaba Trump ya bayyana cewa Iran ta dade tana farautar rayuwarsa domin daukar fansa kan abin da ya yi a baya.
Asali: Legit.ng


