Sakon Khamenei ga Amurka yayin Jana’izar Mahaifinsa bayan Gargadin Trump
- Sabon Jagoran Addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya sha alwashin ɗaukar fansar mutuwar mahaifinsa marigayi Ali Khamenei
- Donald Trump ya ce ya umarci sojojin Amurka su lalata Iran gaba ɗaya idan aka kashe shi, bayan rahotannin yi masa barazana
- Rikicin Iran da Amurka na ci gaba da ƙamari, yayin da ake tattaunawa kan mashigin Hormuz duk da ci gaba da musayar barazana tsakanin ɓangarorin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Sabon Jagoran Addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi alƙawarin ɗaukar fansar mutuwar mahaifinsa.
An hallaka tsohon jagoran Iran, marigayi Ayatollah Ali Khamenei a karshen watan Fabrairun shekarar 2026 daga Amurka da Isra'ila.

Source: Facebook
Alwashin da Mojtaba Khamenei ya yi
A cikin saƙon ta'aziyya da kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran suka wallafa, Mojtaba ya ce za su rama jinin jagoran da aka kashe tare da sauran waɗanda suka mutu, cewar NBC News.
Ya ce ɗaukar fansa shi ne muradin al'ummar Iran, yana mai ƙara da cewa nan ba da jimawa ba mutane masu son 'yanci za su aiwatar da wannan aiki.
Mojtaba, wanda bai fito bainar jama'a ba tun bayan fara yaƙin, bai halarci jana'izar mahaifinsa ba, sai dai ya aika saƙon ta rubuce.
Gargadin da Trump ya yi ga Iran
A gefe guda, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargaɗi ga Iran da kada ta yi yunƙurin kashe shi bayan an ga allunan da ke kira a kashe shi.
Trump ya ce ya ba sojojin Amurka umarni cewa idan aka kashe shi, za su lalata dukkan yankunan Iran gaba ɗaya cikin martani.
Ya kuma kammala saƙonsa da kalmar “Praise be to Allah”, wadda ya riƙa amfani da ita a lokutan yaƙin, abin da ya jawo suka daga wasu ƙungiyoyi.
Ayatollah Ali Khamenei ya mutu ne sakamakon harin sama da aka kai ranar 28 ga Fabrairu, kuma an binne shi ne bayan kwanaki shida na zaman makoki.
Rahotanni sun ce Mojtaba Khamenei ya samu munanan raunuka a harin, ko da yake gwamnatin Iran ba ta tabbatar da hakan ba, kuma ba a gan shi a fili ba.

Source: Getty Images
Dangantaka n akara tsami tsakanin Iran, Amurka
Ana ci gaba da fuskantar tsamin dangantaka tsakanin Amurka da Iran, bayan hare-hare da aka yi a mashigin Hormuz da kuma matakan ramuwar gayya daga ɓangarorin biyu.
Masu shiga tsakani daga Qatar sun gana da jami'an Iran domin tattauna bude mashigin Hormuz, yayin da Iran ke neman cikakken iko da hanyar ruwa, cewar CNN.
Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, zai gana da takwaransa na Oman domin tattauna lamarin, yayin da ya zargi Amurka da karya yarjejeniyar wucin gadi kan takunkumin man fetur.
Iran ta yi fatali da mika wuya
An ji cewa kakakin majalisar dokokin Iran kuma jagoran tawagar tattaunawar sulhu ya ce ƙasarsa ba za ta taɓa miƙa wuya ga Amurka ba.
Mohammad Bagher Ghalibaf ya yi barazanar martani idan Amurka ta karya yarjejeniyar da kasashen biyu suka rattaba hannu.
Wani masani ya ce har yanzu akwai yiwuwar a farfaɗo da yarjejeniyar tsakanin Amurka da Iran domin kawo karshen rikicin Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng

