'Mayaudara ne': Trump Ya Bayyana Halin da Ake ciki game da Yarjejeniya da Iran
- Shugaban kasar Amurka, Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran ta ƙare
- Trump ya zargi shugabannin Iran da yaudara, yana mai cewa ba ya son ci gaba da tattaunawa, duk da barin masu shiga tsakani su ci gaba
- Babban sakataren NATO Mark Rutte ya goyi bayan harin Amurka kan Iran, yayin da Trump ya soki ƙawayen NATO saboda ƙin taimakawa Amurka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Shugaban Amurka Donald Trump ya yi magana game da yarjejeniyar kasar da Iran.
Trump ya bayyana cewa yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran ta ƙare bayan sabbin hare-hare tsakanin ɓangarorin biyu.

Source: Facebook
Trump ya yi waɗannan kalamai ne bayan Amurka ta kai hare-hare kan Iran cikin dare, yayin da dakarun Iran suka ce sun kai hari sansanonin Amurka, cewar The Guardian.
Trump ya gaji da hulda da Iran
Bayan kalaman Trump, farashin ɗanyen mai ya yi tashin kusan kashi biyar cikin ɗari saboda fargabar ƙarin rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.
Da yake jawabi a taron NATO da aka gudanar a Ankara, Trump ya ce ba ya son ci gaba da hulɗa da Iran.
Ya zargi shugabannin Iran da munanan halaye, yana mai cewa idan suka mallaki makamin nukiliya za su yi amfani da shi.
Trump ya ce a ganinsa batun tsagaita wutar ya ƙare gaba ɗaya, kuma ba ya ganin amfani cikin ci gaba da tattaunawa.
Sai dai ya bayyana cewa zai tattauna da Steve Witkoff da Jared Kushner, waɗanda ke jagorantar tattaunawa da Iran.

Source: Getty Images
Trump ya zargi Iran da rashin cika alkawari
Duk da haka, Trump ya jaddada cewa Iran ce ya kamata ta dawo teburin tattaunawa idan har tana son warware rikicin.
Ya ce ba ya son ɓata lokaci wajen tattaunawa da Iran, yana mai zarginsu da karya da rashin cika alkawari.
Trump ya kuma zargi Iran da musanta yarjejeniyar da aka cimma kan hana mallakar makamin nukiliya bayan sun fita wajen manema labarai.
Ya ce wannan hali ya nuna akwai matsala a shugabancin Iran, saboda suna sauya bayanansu bayan kammala tattaunawa.
Babban sakataren NATO, Mark Rutte, ya goyi bayan hare-haren Amurka, yana mai cewa matakin ya zama dole kuma ya dace.
Sai dai duk da goyon bayan Rutte, Trump ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda NATO ba ta taimaka wa Amurka ba.
Ya ce Birtaniya, Jamus da Faransa sun ƙi shiga yaƙin da Iran, suna cewa za su taimaka ne bayan rikicin ya ƙare, cewar rahoton Punch.
Sojojin Amurka sun bayyana cewa sun kai hare-hare kan fiye da wurare 80, ciki har da kwale-kwalen yaƙin Iran, bayan hare-haren da aka kai kan jiragen ruwa a mashigar Hormuz.
Iran ta cilla bama-bamai kan Amurka
Kun ji cewa Iran ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wuta bayan hare-haren da sojojin Amurka suka kai a wasu sassan yankinsu.
Sojojin Amurka sun bayyana cewa harin martani ne bayan Iran ta kai hari kan jiragen kasuwanci uku da ke bi ta mashigar Hormuz.
Wannan musayar wuta ta sake kamari yayin da Iran ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a Bahrain da Kuwait bayan farmakin Amurka.
Asali: Legit.ng

