Tsohon Sarkin Qatar da Ya Daga Darajar Kasar a Duniya Ya Rasu Yana da Shekaru 74
- Rahotanni sun tabbatar da rasuwar tsohon Sarkin Qatar, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani bayan shafe shekaru yana mulki
- Majiyoyi sun ce basaraken da ya ba da gudummawa sosai a kasar ya rasu yana da shekara 74 a duniya
- A mulkinsa, Qatar ta samu gagarumin ci gaba ta hanyar fitar da iskar gas, abin da ya kara mata arziki tare da karfafa matsayinta a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Doha, Qatar - An shiga jimami a kasar Qatar bayan sanar da rasuwar tsohon Sarkin wanda ya kawo ci gaba.
Tsohon Sarkin Qatar, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani, ya rasu yana da shekara 74 a duniya.

Source: Getty Images
Fadar masarautar Qatar ta sanar da rasuwarsa a ranar Lahadi 12 ga watan Yulin shekarar 2026, cewar rahoton Al Jazeera.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya garzaya wurin Kashim Shettima bayan Tinubu ya zaɓi abokin takara a 2027
Lokacin da marigayin ya mulki Qatar
Sheikh Hamad ya shugabanci Qatar daga shekarar 1995 zuwa 2013 wanda ya kawo ci gaba sosai a kasar.
Bayan haka ya sauka daga mulki tare da mika ragamar jagoranci ga dansa na hudu, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, wanda shi ne Sarkin Qatar na yanzu.
Sanarwar ta ce:
"Cikin jimami mai cike da imani da yarda da ƙaddarar Allah da hukuncinsa, Fadar Amiri (Amiri Diwan) na jimamin wannan babban rashi da ya samu ƙasa sakamakon rasuwar Mai Martaba Sarkin Uba, Sheikh Hamad bin Khalifa Al Thani. Allah Ya jiƙansa da rahama. Ya rasu da safiyar yau."

Source: Getty Images
Ci gaban da Qatar ta samu lokacin marigayin
A lokacin mulkinsa, Qatar ta samu babban ci gaba wajen hakowa da fitar da iskar gas mai ruwa (LNG). Wannan ya samar wa kasar dimbin kudaden shiga tare da kara mata tasiri a fagen duniya.
Sakamakon wannan ci gaba, Qatar ta zama daya daga cikin kasashen da suka fi arziki idan aka kwatanta yawan kudin shiga da adadin al'umma, cewar Anadolu.

Kara karanta wannan
Fitaccen 'dan ƙwallo ya mutu kwanaki kadan bayan cire ƙasarsa a gasar Kofin Duniya na 2026
Sheikh Hamad ya kuma jagoranci yunkurin da ya kai ga nasarar Qatar wajen samun damar karbar bakuncin gasar cin Kofin Duniya ta FIFA ta shekarar 2022.
An sanar da wannan nasara ne a shekarar 2010, lamarin da ya bude kofar aiwatar da manyan ayyukan gine-gine da zuba jari a fadin kasar.
Wadannan ayyuka sun canza fasalin birnin Doha sosai, inda aka gina sababbin hanyoyi, gine-ginen zamani da sauran muhimman abubuwan more rayuwa.
Ana kallon gudunmuwar Sheikh Hamad a matsayin daya daga cikin manyan abubuwan da suka sauya Qatar zuwa kasa mai karfin tattalin arziki da tasiri a duniya.
Sarkin Qatar ya yi waya da Donald Trump
A baya, kun ji cewa Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani ya yi magana da Shugaba Donald Trump ta wayar salula kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.
Fadar Sarkin Qatar ta tabbatar da tattaunawar shugabannin kasashen biyu, inda ta jero muhimman batutuwan da suka tabo musamman game da Gabas ta Tsakiya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin sake shirya tattaunawa tsakanin Amurka da Iran a karo na biyu a birnin Islamabad.
Asali: Legit.ng