Buhari zai hadu da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Althani

Buhari zai hadu da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Althani

A yau da safiyar 23 ga Watan Afrilun 2019 ne mu ka samu labari cewa Sheikh Tamim bin Hamad Althani na Kasar Qatar zai kawo ziyara Najeriya inda zai halarci wani taro har ya gana da shugaban kasa.

Kamar yadda labari ya zo mana daga fadar shugaban kasar, Mai girma Sheikh Tamim bin Hamad Althani zai halarci taron nan da kungiyar OPEC ta kasashen da ke fitar da man fetur ta shirya wannan karo a cikin Garin Abuja.

Mai magana a madadin shuaban kasa watau Garba Shehu ya kuma tabbatar da cewa shugaba Hamad bin Khalifa na II zai gana da Takawaransa shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa a wannan ziyara da zai kawo.

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya ta samu Biliyan 300 ta hannun Jami'an Kwastam

Buhari zai hadu da Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Althani
Shugaban Najeriya Buhari zai zauna da Tamim bin Hamad II
Asali: Twitter

Wannan zama da za ayi tsakanin shugaban Najeriya da Hamad bin Khalifa na Qatar shi ne zama na biyu da shugabannin za su yi a cikin shekara 2, bayan sun hadu a shekarar bara. A 2016 kuma shugaba Buhari ya leka kasar ta Qatar.

A lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyara zuwa kasar Qatar, kusan shekaru uku da su ka wuce, yayi magana a game da farashin man fetur inda ya nemi kasashen OPEC da sauran kasashe masu arzikin mai da su hada kai.

Idan ba ku manta ba, a karshen bara ne kasar ta Qatar ta tabbatar da cewa za ta fice daga cikin kungiyar OPEC bayan ta shafe shekaru kusan 60 ana damawa da ita. Qatar ita ce kasar da ta fi kowace kasa a Duniya fitar da arzikin gas.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel