Iran Ta Nuna Yatsa ga Donald Trump, Ta Harba Makamai kan Kuwait da Wasu Kasashe 2

Iran Ta Nuna Yatsa ga Donald Trump, Ta Harba Makamai kan Kuwait da Wasu Kasashe 2

  • Sojojin Amurka sun kai hari kan wuraren adana makamai da jiragen sama na Iran a bakin tekun a daren Laraba, 8 ga Yulin 2026
  • Rundunar IRGC ta Iran ta kai hari kan sansanonin sojin Amurka da ke Kuwait, Bahrain da Qatar a matsayin ramuwar gayya
  • Jordan ta harbo makamai guda takwas na Iran a sararin samaniyarta kafin su sauka ƙasa, yayin da Iran ta yi gargadi ga kasar Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Iran - Amurka da Iran sun ci gaba da musayar hare-hare karo na biyu a jere, lamarin da ya jefa yarjejeniyar tsagaitar wuta da ƙasashen biyu suka cimma a watan Afrilu a cikin mawuyacin hali.

Rundunar tsaron Amurka ta CENTCOM ta sanar a dare na Laraba cewa sojojinta sun farmaki wurare kusan 90 a bakin tekun Iran, ciki har da wuraren ajiya na makamai da jiragen sama marasa matuƙa, da kuma wuraren kaya da kayayyaki.

Kara karanta wannan

"Za mu rama sau 20"; Shugaba Trump ya yi sabuwar barazana ga Iran

Iran ta harba makamai kan sansanonin sojin Amurka da ke a kasashen 3 na Gabas ta Tsakiya.
Shugaba Donald Trump (hagu) da wani bangare na kasar Iran da ke ci da wuta. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kafar watsa labaran Aljazeera ta ruwaito CENTCOM ta ce manufar harin ita ce ta lalata ikon Iran na toshe hanyar jigilar kayayyaki ta Tekun Hormuz.

Iran ta kai hare-hare kasashe 3

Shugaba Donald Trump ya wallafa a shafin Truth Social cewa harin na Amurka shi ne ramuwar gayya ga "harin da Iran ta kai wa jiragen ruwa jiya," yana mai cewa za su sake kai munanan hare-hare idan Tehran ta sake yin wani kuskuren.

Hare-haren Laraban suna zuwa ne a gaban wanda Amurka ta kai wa Iran ranar Talata, inda ta lalata wurare fiye da 80 sakamakon Iran ta kai wa jiragen ruwa na kasuwanci hari a Tekun Hormuz.

A mayar da martani, Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta sanar da Alhamis cewa ta kai hari kan sansanonin da sojojin Amurka ke amfani da su a Kuwait da Bahrain.

Kara karanta wannan

Farashin mai ya haura Dala 80 bayan Trump ya sake rura rikicin Iran

Bayan haka, sojojin Iran sun ce sun kai hari kan tsarin makamai na Patriot a Kuwait, na'ura mai karɓar siginar tauraron dan adam a Qatar, da kuma ɗakunan ajiyar mai na Amurka a Bahrain.

Matakin da kasashen suka dauka

Ma'aikatar Tsaro ta Kuwait ta tabbatar da cewa aƙalla mutum ɗaya ya ji rauni sakamakon harin. Qatar ta ɗauki matakin kariya ta tsaro amma ta soke shi jim kaɗan bayan haka, cewar rahoton Sky News.

Rundunar soji ta Jordan kuma ta sanar da cewa ta tarwatsa makamai guda takwas na Iran da suka wuce sararin samaniyar ƙasar, ta ƙara da cewa gutsuttsura da suka faɗo ƙasa ba su cutar da kowa ba.

Iran da Amurka na ci gaba da kai wa juna hari kan mashigar Hormuz
Wani jirgin dakon mai yana ci da wuta bayan an farmake shi a mashigar Hormuz. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Batun Tekun Hormuz

Babban mai sasantawa na Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya bayyana cewa ba za su sake bude Tekun Hormuz ba har sai dai a ƙarƙashin "shirye-shiryen Iran" yana mai cewa za su kai hari idan aka farmake su.

Wannan tashin hankali yana barazana ga wata yarjejeniyar da ƙasashen biyu suka cimma a watan da ya gabata don tsagaitar wutar da kuma sake buɗe Tekun Hormuz ga jigilar kaya ta duniya.

Kara karanta wannan

Daga fara kai hari, Amurka ta yi wa sojojin kasar Iran mummunar ɓarna

Amurka ta kai hare-hare Iran

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Amurka ta kai hari mai karfi kan Iran bayan da wasu jiragen ruwa uku na kasuwanci suka fuskanci hare-hare a mashigar Hormuz a ranar Talata.

Bayan labarin ya bazu, hukumar watsa labarai ta jihar Iran ta bayyana cewa an kai hari kan tsibirin Qeshm da birnin Bandar Abbas da kauyen Sirik, inda wasu mutane suka jikkata.

Rundunar sojin Amurka ta farmaki Iran ne a daidai lokacin da jama'ar kasar ke jana'izar Ayatollah Ali Khamenei da aka kashe a ranar 28 ga Fabrairun 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com