Wasu Yahudawa mazauna Ingila sunyi Allah wadai ga kasar Isra'ila

Wasu Yahudawa mazauna Ingila sunyi Allah wadai ga kasar Isra'ila

A wata ziyara da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kai kasar Ingila, wani babban malamin Yahuduwa, Elahanan Beck da wasu 'yan tawagarsa na shiyyar Yahudawan Ortodox wadanda suke bin darikar "Neturei Karta" sun kaiwa shugaba Erdoğan ziyara, domin yi masa jinjina game da irin namijin kokarin da yake yi na gasawa shugabannin Isra'ila aya a hannu

Wasu Yahudawa mazauna Ingila sunyi Allah wadai ga kasar Isra'ila
Wasu Yahudawa mazauna Ingila sunyi Allah wadai ga kasar Isra'ila

A wata ziyara da shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kai kasar Ingila, wani babban malamin Yahuduwa, Elahanan Beck da wasu 'yan tawagarsa na shiyyar Yahudawan Ortodox wadanda suke bin darikar "Neturei Karta" sun kaiwa shugaba Erdoğan ziyara, domin yi masa jinjina game da irin namijin kokarin da yake yi na gasawa shugabannin Isra'ila aya a hannu.

DUBA WANNAN: Labari mai dadi: Gwamnatin Tarayya ta bada aikin hanyar Kano zuwa Bauchi

Bayan zaman da suka yi da shugaba Erdoğan malamin Yahuduwan Beck ya yiwa manema labarai jawabi a birnin Landan, inda yace,

"Tallafawa Yahudawan Sahyoniyawan da Isra'ila keyi mugun abune ga al'umar Yahudu. Idan kuna son ku taimaka wa Yahudawa to ku gaggauta goya wa shugaba Erdoğan baya".

Da yake magana akan shugabannin kasar Amurka da kuma kasar Ingila, Beck yace,

"Duk kasar data tallafa wa kasar Isra'ila, to ta san cewa ta cutar da al'ummar Yahudawa".

Beck yace, matsalar Isra'ila ba wai iya kan Falasdinawa kawai ta tsaya ba, a yau Isra'ila kasace mai hatsari babba ga al'ummar Yahudawa.

"Idan kuna son ku taimakawa al'ummarYahudawa to ku gaggauta goya wa shugaba Erdoğan baya. Ku yi gaggawar janye jakadojinku daga kasar Isra'ila. Ku fita daga kasar Isra'ila. Ku zama tsintsiya madaurinki daya don tunkarar ta. Muna Allah wadai da wutar tashin hankalin dake cigaba da ruruwa babu kakkautawa a yankunan da abin ya shafa. Muna son zaman lafiya ya dawo yankunan da basa cikin hayyacin su. A kullum addu'ar da muke shine Allah ya tarwatsa kasar Isra'ila. Bamu son kasashe biyu. Fatanmu kasa daya tilo, watau kasar Falasdinu. Muna son Falasdinawa su dawowa gida. Yahudawa da al'ummar Musulmai muna iya rayuwa tare kamar a baya, kafin zuwan azzaluman Sahyoniyawa".

Yahudawan Ortodox al'ummar Yahudawa ne mazauna kasar Ingila wadanda suke bin darikar "Neturei Karta". Sun jima suna nuna rashin goyon bayan su akan irin bakin zaluncin da kasar Isra'ila take yi akan al'ummar Falasdinawa, inda suke ikirarin cewar su basu san da wata kasar Isra'ila ba, iya kasar Falasdin suka sani tun farko, wacce suke zaman su lafiya da al'ummar Musulmi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng