Abubuwan da Mutane Ba Su Fahimta ba game da Jana'izar Ayatollah Khamenei

Abubuwan da Mutane Ba Su Fahimta ba game da Jana'izar Ayatollah Khamenei

Birnin Tehran, Iran - An fara gudanar da jana'izar tsohon jagoran addinin ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya rasu watanni da suka gabata.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Hukumomi a kasar Iran sun shirya cewa za a ɗauki aƙalla kwanaki bakwai ana gudanar da tarukan jana'izar a fadin biranen ƙasar.

Ana gudanar da jana'izar Khamenei a Iran
Gawar Khamenei da ta wasu iyalansa ana zagaya da su a birnin Tehran Hoto: Atta Kenare
Source: Getty Images

Legit Hausa ta fahimci cewa Ayatollah Ali Khamenei ya rasa ransa ne sakamakon wani harin haɗin gwiwar Isra'ila da Amurka a kan gidansa ranar 28 ga watan Fabrairun 2026.

Meyasa aka jinkirta jana'izar Khamenei?

Tun bayan da aka kashe Ayatollah Ali Khamenei ba a gudanar da jana'izarsa ba, saboda dalilai na tsaro.

Hukumomi a Iran sun jinkirta gudanar jana'izar tsohon jagoran addinin ne har na tsawon wata huɗu sakamakon yaƙin da aka ci gaba da gwabzawa tsakanin kasar da Amurka da kuma Isra'ila.

Kara karanta wannan

2027: Maza da mata sun fito gangamin nuna goyon baya ga tazarcen Tinubu a Kwara

Biranen da za a gudanar da jana'izar Khamenei

An dai tsara cewa za a fara jana'izar Ali Khamenei ne daga ranar Juma'a, 3 ga watan Yulin 2026 zuwa 9 ga watan Yulin 2026, inda za a kwashe kwanaki bakwai ana yi, rahoton Aljazeera ya nuna hakan.

Za a gudanar da jana'izar ne a biranen Tehran, Qom, Mashdad, Najaf da qarbala da ke a kasashen Iran da Iraki.

An fara jana'izar ne a birnin Tehran, a babban masallancin Juma'a na birnin domin inda jama'a suka yi bankwana da gawar marigayi Ayatollah Ali Khamenei.

Bayan birnin Tehran, an wuce da gawar Khamenei zuwa birnin Qom wanda yake zama babban birnin mazhabin Shia na duniya.

Daga birnin Qom, za a wuce da gawar Ali Khamenei zuwa kasar Iraki inda za a yi bukukuwa jana'izar a biranen Najaf da Karbala a ranar Laraba, 8 ga watan Yulin 2026.

Daga Najaf da Karbala za a mayar da gawar zuwa Iran domin jana'izar ƙarshe, wadda aka tsara za a yi ranar Alhamis, 9 ga Yuli a Haramin Imam Reza da ke Mashhad.

Kara karanta wannan

Lamuran siyasa 6 da ka iya tasiri a zaɓen Najeriya na shekarar 2027

Marigayi Ayatollah Ali Khamenei dai ya kasance haifaffen birnin Mashdad inda a nan ne kuma za a binne gawarsa.

Meyasa ba za a ga Mojtaba Khamenei ba?

Sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei ba zai halarci jana'izar mahaifinsa ba.

Mojtaba Khamenei dai ba a gan shi a bainar jama'a ba tun bayan da aka nada shi sabon jagoran addini na kasar Iran.

Dalilai na tsaro ne suka sanya Mojtaba Khamenei ba zai halarci jana'izar ba domin ka da a yi yunkurin farautar rayuwarsa.

Ana janaizar Khemenei a Iran
Dubun dubutar mutane a wurin janaizar Ayatollah Ali Khamenei Hoto: AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Su wa ke samar da tsaro?

Rundunar tsaro ta Basij ce ke jagorantar tsara shirin jana'izar. Ta bayyana cewa ta gudanar da wasu sauye-sauye a biranen da ake yin jana'izar, tashar BBC Hausa ta kawo rahoton.

Rundunar ta ce mayar da manyan titunan ƙasar wuraren ajiye motoci, yayin da masallatai da makarantu da filayen wasanni da jami'o'i suka kasance wuraren kwana ga mutane a tsawon lokacin jana'izar.

Hakazalika, rundunar dakarun juyin juya halin ƙasar, watau IRGC ce ke da ikon samar da tsaro a manyan biranen Iran yayin jana'izar marigayi Ayatollah Ali Khamenei.

Kara karanta wannan

2027: Malami ya gana da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a Abuja

Khamenei ya ja kunnen mutanen Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa sabon jagoran addini na kasar Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi muhimmin kira ga mutanen kasar.

Mojtaba Khamenei, ya yi kira ga al'ummar ƙasar da su ƙarfafa haɗin kai tare da kauce wa duk wani abu da zai iya haddasa rabuwar kai a tsakanin jama'a.

Khamenei ya jaddada cewa haɗin kai tsakanin jama'a shi ne babban abin da zai taimaka wa Iran wajen tunkarar duk wata barazana daga maƙiyanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng