Lauya Ya Bayyana Babbar Barazanar da Tinubu Ke Fuskanta a Yunkurin Tazarce

Lauya Ya Bayyana Babbar Barazanar da Tinubu Ke Fuskanta a Yunkurin Tazarce

  • Lauya kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama, Deji Adeyanju, ya bayyana babbar barazanar da ke tunkarar Shugaba Tinubu kan tazarce
  • Adeyanju ya danganta hasashensa da yanayin siyasa da ra'ayin al'ummar Arewacin Najeriya, yana mai cewa hakan ba alama ce mai kyau ga APC ba
  • Kalaman nasa sun fito ne a daidai lokacin da kotu ta soke shugabancin ADC ƙarƙashin David Mark da tsarin da ya samar da Atiku a matsayin ɗan takarar jam'iyyar na 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja – Fitaccen lauya kuma mai fafutukar kare haƙƙin bil'adama, Deji Adeyanju, ya bayyana babbar barazanar da Shugaba Bola Tinubu yake fuskanta a yunkurinsa na yin tazarce.

Adeyanju ya bayyana tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin babban ƙalubalen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke fuskanta wajen neman wa'adin mulki na biyu a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Amaechi ya hango abin da zai haddasa yakin basasa a Najeriya ana batun zaben 2027

Adeyanju ya yi magana kan tazarcen Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na jawabi a wajen kamfen din APC a Kaduna Hoto: Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Me lauya ya hasaso kan Tinubu?

Adeyanju ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, wanda a baya ake kira Twitter, ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026.

Ya danganta hasashensa da yanayin siyasa da ra'ayin al'ummar Arewacin Najeriya, yana mai cewa hakan na iya zama babbar matsala ga jam'iyyar APC mai mulki yayin tunkarar zaɓen 2027.

A cikin saƙon nasa, Adeyanju ya rubuta cewa:

“Atiku ne babban ƙalubalen da Tinubu ke fuskanta wajen sake lashe zaɓe. Duk wanda ya fahimci tarihin siyasar Najeriya ya san da haka. Yanayin siyasa da ra'ayin al'ummar Arewacin Najeriya ba sa nuna alamar samun nasara ga jam'iyyar da ke mulki.”

Kalaman Adeyanju sun ƙara shiga cikin muhawarar da ake yi kan ƙarfin jam'iyyun adawa da rawar da Atiku zai taka a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Matsalar shari'a ta dabaibaye takarar Atiku a ADC

Bayyanar wannan ra'ayi na Adeyanju ta zo ne a ranar da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke hukuncin da zai iya kawo cikas ga shirin siyasar Atiku.

Kara karanta wannan

Sama da kasa ba za su hade ba idan aka hana Atiku takara in ji ministan Tinubu

Kotun ta soke tsarin shugabancin jam'iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark.

Haka kuma, ta soke matakan cikin gida da jam'iyyar ta bi wajen zaɓen Atiku a matsayin ɗan takararta na shugaban ƙasa.

Kotun ta kuma umarci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) da kada ta amince da duk wani mataki da aka ɗauka a taron kwamitin zartarwa na ƙasa na ADC da ake takaddama a kai.

Tsohon mataimakin shugaban ADC na ƙasa, Nafiu Bala Gombe, ne ya shigar da ƙarar, inda ya ƙalubalanci sahihancin tsarin shugabancin jam'iyyar.

Deji Adeyanju ya yi magana kan zaben 2027
Deji Adeyanju na jawabi a wajen taro Hoto: Adeyanju Deji
Source: Twitter

Abin da INEC za ta yi kan Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ce ba za ta ɗauki matsaya kan rikicin shugabancin jam'iyyar ADC ba, har sai ta samu tare da nazarin sahihin kwafin hukuncin kotu.

INEC ta ce ba za ta yanke hukunci bisa rahotannin kafafen yaɗa labarai ba, saboda akwai yiwuwar bayanan da aka wallafa ba su yi daidai da abin da kotu ta yanke ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng