An Sanya Dokar Hana Fita a Taraba, an Kashe Dan Sanda bayan Kisan Makiyayi

An Sanya Dokar Hana Fita a Taraba, an Kashe Dan Sanda bayan Kisan Makiyayi

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa wata karamar hukuma a jihar Taraba ta sanya dokar hana fita ta dare
  • Hakan ya biyo bayan kisan dan sanda yayin da wasu fararen hula uku suka ji rauni bayan harin wasu mahara a Gembu
  • 'Yan sanda sun tura jami'ai domin dawo da zaman lafiya, yayin da ake bincike kan hare-haren biyu da suka girgiza Taraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gembu, Taraba - Wani ɗan sanda ya rasu, yayin da fararen hula uku suka samu raunuka sakamakon harin wasu 'yan bindiga.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa amarin a faru ne garin Gembu, hedikwatar karamar hukumar Sardauna ta Taraba.

An kashe dan sanda bayan harbe makiyayi
Taswirar jihar Taraba da aka samu rikicin manoma da makiyaya. Hoto: Legit.
Source: Original

Hare-haren sun zo ne yayin da matsalolin tsaro suka sake ƙamari a Taraba, inda aka kuma samu wani mummunan rikici a karamar hukumar Bali a wannan rana, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi ta'asa a Kogi, sun hallaka mutane da dama yayin hari

Taraba: Musabbabin sanya dokar hana fita

Rahotanni sun bayyana cewa karamar hukumar Sardauna ta sanya dokar hana fita da dare a Gembu bayan harin da ya yi sanadin mutuwar ɗan sandan.

An ce shugaban karamar hukumar, Hon. J. Umar, ne ya bayar da umarnin sanya dokar ta wata wasiƙa mai kwanan watan 6 ga Yuli, 2026.

Daraktan Gudanarwa da Harkokin Gabaɗaya na karamar hukumar, Mista Eric Mathew Vakude, ne ya sanya hannu kan wasiƙar da ta sanar da dokar.

Sabuwar dokar ta hana zirga-zirga a cikin garin Gembu daga ƙarfe tara na dare zuwa ƙarfe biyar na safe har sai an ba da wani sabon umarni.

Sanarwar ta ce an ɗauki matakin ne domin kare rayuka da dukiyoyi tare da tabbatar da zaman lafiya a yankin.

An sanya dokar hana fita a wani yankin Taraba
Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba da kwamishinan yan sanda, Moorkwap Sebastian Dongshal. Hoto: Taraba State Police Command.
Source: Facebook

Manoma 10 sun raunana a rikicin makiyaya

A wani lamari dabam, wani makiyayi ya mutu yayin da manoma sama da 10 suka samu munanan raunuka a rikicin manoma da makiyaya a ƙauyen Pangri.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kori mutanen kauyuka 30 a Sokoto, manya sun dauki mataki

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan shanu sun lalata gonar wani manomi, lamarin da ya tayar da saɓani.

An ce mamallakin gonar ya gayyaci wani ɗan sanda domin kama mamallakin shanun, amma makiyayin ya ƙi amincewa da kama shi.

Rahotanni sun ƙara da cewa ɗan sandan ya harbi makiyayin yayin da yake ƙoƙarin tserewa ko kuma yaƙi da kama shi.

Bayan faruwar lamarin, wasu makiyaya daga maƙwabtan ƙauyuka sun haɗu suka kai farmaki kan manoman domin ramuwar gayya.

Majiyoyi sun ce manoma sama da 10 sun samu munanan raunuka, yayin da aka kuma ƙone gidaje da dama mallakin manoman.

Wani mazaunin ƙauyen, Dauda Pangri, ya bayyana cewa rikicin ya faru ne ranar kasuwa, lamarin da ya sa 'yan kasuwa suka tsere.

Ya ce an garzaya da waɗanda suka ji raunuka zuwa Babban Asibitin Bali domin samun kulawar likitoci.

Kansila da mutum 10 sun mutu a Taraba

An ji cewa akalla mutane 10 suka rasa rayukansu bayan barkewar rikicin kabilanci a jihar Taraba da ke Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Daga taimako, ƴan bindiga sun bindige tsohon sojan Najeriya kusa da Abuja

Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da kansila mai ci a rikici tsakanin manoma da makiyaya a Gundom, karamar hukumar Donga.

Rahotanni sun ce rikicin ya fara ne bayan wani makiyayi ya shigar da shanunsa gona, inda aka kama shi daga bisani aka kashe shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.