Mojtaba Ya Fadi dalilin da Ya Sa ba Zai Halarci Jana’izar Mahaifinsa, Khemenei ba
- Wani babban jami'in jagoran addinin Iran ya ce Mojtaba Khamenei ba zai halarci jana'izar mahaifinsa ba saboda matsanancin barazanar tsaro
- • Iran na shirya jana'izar Ayatollah Ali Khamenei tare da tarurrukan makoki na kwanaki, yayin da dubban mutane ke shirin halarta daga ciki da wajen ƙasar
- • Tsohon ministan harkokin wajen Indiya Salman Khurshid zai halarci jana'izar domin isar da saƙon ta'aziyya da nuna goyon bayan ƙasarsa ga Iran
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tehran, Iran - Wani babban wakilin Jagoran Addini na Iran a Indiya, Ayatollah Hakim Elahi, ya yi magana game da shirin birne Ayatollah Ali Khamenei.
Elahi ya bayyana cewa Mojtaba Khamenei ba zai fito bainar jama'a domin halartar jana'izar mahaifinsa, marigayi Ali Khamenei ba saboda matsalolin tsaro.

Source: Getty Images
Hakan na cikin wata hira da ya yi da India Today kafin tafiyarsa zuwa Tehran daga filin jirgin saman New Delhi.
Elahi ya ce hukumomi ba za su iya tabbatar da tsaron Mojtaba ba, musamman yayin da rikici da Isra'ila ke ci gaba da ƙamari.
Ya ce ya gana da wasu mutane da suka sadu da Mojtaba a Iran, kuma sun bayyana masa cewa yana son fitowa ya gana da jama'a, amma jami'an tsaro sun hana hakan saboda haɗarin da ke tattare da lamarin.
Elahi ya ƙara da cewa Iran na cikin makoki tun bayan rasuwar Ayatollah Ali Khamenei, inda mabiyansa ke kallon mutuwarsa a matsayin babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba.
Ya bayyana cewa mutane daga sassa daban-daban na Iran da kuma ƙasashen waje na ci gaba da zuwa domin halartar jana'izar tare da nuna goyon baya ga marigayin da kuma alkawarin ci gaba da bin tafarkinsa.

Source: Getty Images
Hukumomin Iran na sa ran jana'izar za ta tara dimbin jama'a domin nuna goyon baya ga Jamhuriyar Musulunci bayan rikicin da aka yi, tare da shirya jerin gwanon makoki a birane da dama.
Da aka tambaye shi game da barazanar Isra'ila na ƙarin hare-hare, Elahi ya ce Iran ta fito daga rikicin cikin ƙarfi, yana mai cewa ƙasashe da dama sun bayyana cewa Iran ce ta yi nasara.
A wani ɓangaren kuma, tsohon Ministan Harkokin Wajen Indiya, Salman Khurshid, ya ce zai je Tehran domin wakiltar jam'iyyar Congress da kuma isar da wasiƙar ta'aziyya daga shugaban jam'iyyar, Mallikarjun Kharge.
Khurshid ya ce Indiya da Iran suna da dangantaka mai ƙarfi tun shekaru masu yawa, don haka ya dace Indiya ta tsaya tare da Iran a wannan lokaci na jimami tare da nuna alhininta kan rasuwar jagoran ƙasar.
Gargadin da Amurka ta yi ga Iran
An ji cewa yayin da ake maganar sulhu tsakanin Amurka da Iran, Shugaba Donald Trump ya gargadi Iran cewa kasar za ta iya sake ɗaukar matakin soja.
Trump ya ce sojojin Amurka sun kai hare-hare kan wuraren ajiyar makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa, tare da cibiyoyin radar da ke bakin teku.
Ya yi barazanar cewa idan Iran ta ci gaba da hare-harenta, Amurka za ta dauki mataki, yana mai cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba za ta ci gaba da wanzuwa ba.
Asali: Legit.ng

