Khamenei Ya Gano Makircin 'Makiya', Ya Ja Kunnen Mutanen Iran
- Jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi gargadin cewa maƙiyan ƙasar na ƙoƙarin haddasa rarrabuwar kai a cikin al'umma
- Ya ce bayan gazawarsu a fagen daga, maƙiyan Iran sun koma amfani da hanyoyin da za su raunana juriyar jama'a da raba kansu
- Mojtaba Khamenei ya buƙaci 'yan ƙasar su haɗa kai tare da guje wa duk wani abu da zai haifar da rashin haɗin kai ko ya kawo rashin kishin kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Ƙasar Iran– Sabon Jagoran Addinin Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei, ya yi kira ga al'ummar ƙasar da su ƙarfafa haɗin kai tare da kauce wa duk wani abu da zai iya haddasa rabuwar kai a tsakanin jama'a.
A cikin wani saƙo da aka karanta a madadinsa ranar Alhamis, 4 ga watan Yuni, 2026, Khamenei ya bayyana cewa maƙiyan Iran na ƙoƙarin cimma wasu manufofi ta hanyar tayar da rashin jituwa.

Kara karanta wannan
Yadda jami'an tsaro suka kai samame Yobe, an gano makerar bindigu da kayan aikinsu

Source: Getty Images
Reuters ta wallafa cewa Khamenei ya ce a halin yanzu barazanar da ƙasar ke fuskanta ba ta tsaya ga rikice-rikicen waje kaɗai ba, domin akwai yunƙurin raunana juriyar al'umma.
Mojtaba Khamenei ya buƙaci haɗin kan al'umma
Al-Jazeera ta wallafa cewa Khamenei ya jaddada cewa haɗin kai tsakanin jama'a shi ne babban abin da zai taimaka wa Iran wajen tunkarar duk wata barazana daga maƙiyanta.
A cewarsa, duk wani mataki ko furuci da zai haddasa rashin haɗin kai, takaici ko jawo rauni a tsakanin jama'a na iya zama wata hanya ta taimakawa maƙiyan ƙasar wajen cimma manufarsu.
Jagoran ya buƙaci 'yan Iran su kasance masu jajircewa tare da nuna goyon baya ga ƙasar domin kare zaman lafiyarta da kuma ci gaban da aka samu.
An karanta saƙon yayin bikin tunawa da Khamenei
An karanta saƙon Khamenei ne a yayin bukukuwan tunawa da cika shekara da rasuwar wanda ya kafa Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Ayatollah Ruhollah Khameini.
Haka kuma taron ya zo daidai da wani babban bikin addinin Shi'a da ake gudanarwa a ƙasar, inda dubunnan mutane suka halarta domin tunawa da muhimman abubuwan tarihi da suka shafi tsarin Jamhuriyar Musulunci.

Source: Getty Images
Kalaman Khamenei na zuwa ne a daidai lokacin da Iran ke ci gaba da fuskantar ƙalubalen siyasa da tsaro a yankin Gabas ta Tsakiya.
Jami'an ƙasar ke yawan zargin wasu ƙasashe da ƙungiyoyi da ƙoƙarin tayar da tarzoma ko kawo cikas ga zaman lafiyar cikin gida.
Sai dai jagoran ya nuna cewa mafi muhimmanci a wannan lokaci shi ne tabbatar da haɗin kai, ƙarfafa gwiwar jama'a da kuma kare muradun ƙasa daga duk wata barazana ta ciki ko ta waje.
Kasar Amurka ta fasa yaki da Iran
A baya, mun ruwaito cewa Shugaban Amurka, Donald Trump, ya shaida wa wasu manyan mataimakansa a sirrance cewa ba zai cigaba da musayar wuta da Iran a fagen daga ba.
Duk da yawaitar arangama a yankin, jami’an sun ce yarjejeniyar dakatar da kai hare-haren sama da aka shafe makonni ana aiwatarwa tana nan daram a tsakanin Amurka da Iran.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Donald Trump ke cewa sun kusa cimma yarjejeniya da Iran domin kawo karshen yakin da suka fara a Fabrairun 2026 gaba daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
