An Jefa Yan Sokoto a Gidan Yarin Abidjan, Gwamnatin Tinubu Ta Ceto Su, 1 Ya Mutu

An Jefa Yan Sokoto a Gidan Yarin Abidjan, Gwamnatin Tinubu Ta Ceto Su, 1 Ya Mutu

  • Gwamnatin Tarayya ta karɓi 'yan Najeriya biyar da aka ceto daga gidan yarin MACA a Côte d’Ivoire bayan cafke su
  • Ministar Harkokin Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu ta ce an tsare su ba tare da tuhuma ko shari'a ba, sannan ta nemi a biya diyya
  • Gwamnatin Tarayya ta roƙi gwamnatin Sokoto ta tallafa wa matasan da aka ceto ta hanyar horas da su sana'o'i

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta karɓi matasan Najeriya shida da aka tsare a gidan yarin MACA da ke Abidjan a Côte d’Ivoire.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa tun a watan Agustan bara ta shekarar 2025 ake rike da su kafin a ceto su ne ta hanyar ƙoƙarin diflomasiyya.

An tsare wasu ƴan Sokoto a Cote d'ivoire
Ministan harkokin waje, Bianca Ojukwu da matasan da aka ceto daga Cote D'Ivoire. Hoto: @Ojukwu_Bianca.
Source: Twitter

Ministar Harkokin Waje, Bianca Odumegwu-Ojukwu ita ta tabbatar da haka a shafinta na X a yau Asabar 4 ga watan Yulin 2026.

Kara karanta wannan

Umarnin da fadar shugaban kasa ta ba DSS, EFCC kan batun ma'aikatar bogi

An daure matasa daga Sokoto a Cote D'Ivoire

Sanarwar ta ce matasan shida, Aliyu Malami, Nasiru Umar, Shamsu Abubakar, Sa'adu Bello, Lyman Mohammed da Usama Murtala sun yi tafiya daga Sokoto zuwa Abidjan domin kasuwanci ta hanya.

An ce hukumomin Côte d’Ivoire sun kama su tare da tsare su a gidan yari ba tare da gurfanar da su a kotu ko yi musu shari'a ba.

Ta ce bayan an kai batun ga ministar a watan Afrilu, ta tuntubi Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Abidjan domin fara ƙoƙarin ceto su.

A cewarta, ci gaba da tattaunawa tsakanin ofishin jakadanci da Ma'aikatar Harkokin Waje ya haifar da nasarar samun sakin matasan.

Sai dai Usama Murtala ya kamu da rashin lafiya sakamakon mawuyacin halin da ake ciki a gidan yarin, kuma rashin kulawar lafiya ya ƙara tsananta halin da yake ciki.

Usama ya rasu a ranar 24 ga Yuni, 2026 a wani asibitin kula da marasa lafiya masu buƙatar kulawa ta musamman, kwana guda bayan hukumomin Côte d’Ivoire sun sake su.

Kara karanta wannan

INEC ta kirkiro shafin rajistar katin zabe ta yanar gizo, ta kara wa'adin mako 2

An birne wani matashi da aka jefa gidan kason Cote d'Ivoire
Taswirar jihar Sokoto da ke Arewacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda aka birne Usama a Abidjan

An birne marigayin washegari bisa tsarin addinin Musulunci bayan tuntubar iyalansa da ke Sokoto.

Ministar Harkokin Waje ta ce ba a sanar da hukumomin Najeriya game da tsare matasan ba, abin da ya jinkirta shiga tsakani ta hanyar diflomasiyya.

Bianca Odumegwu-Ojukwu ta ce ba a gabatar da takardar tuhuma a kansu ba, kuma ba a kai su kotu domin yi musu shari'a ba.

Ta danganta wahalar da suka sha da matsalar harshe, tana mai cewa ba su iya sadarwa da kyau a ƙasar da ake amfani da harshen Faransanci.

Ta ce rashin iya magana da Turanci ko Faransanci ya hana su samun lauya ko damar kare kansu yadda ya kamata.

Ministar ta ce matakin ceto matasan ya yi daidai da manufar diflomasiyyar kare 'yan ƙasa ƙarƙashin shirin Sabuwar Fata na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ta roƙi gwamnatin jihar Sokoto ta samar wa matasan damar gyaran rayuwa da koyon sana'o'i domin su sake tsayawa da ƙafafunsu.

Kara karanta wannan

2027: Malami ya gana da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a Abuja

Ɗaya daga cikin waɗanda aka ceto, Aliyu Malami, ya ce ya tafi Côte d’Ivoire ne domin kasuwanci amma ya ƙare a gidan yari cikin mawuyacin hali.

Yadda aka kori minista daga gidan ubanta

An ji cewa Bianca Odumegwu-Ojukwu ta tuna baya kan irin gwagwarmayar da ta sha a baya a rayuwarta lokacin da take matashiya.

Ministar harkokin wajen ta Najeriya ta bayyana akwai lokacin da mahaifinta ya taɓa korarta daga gida saboda ta shigar gasar kyau.

Ta nuna muhimmancin ilmi ga rayuwar mace inda ta ba da shawarar cewa ka da ƴan mata su riƙa kyale karatu bayan sun fara samun kuɗi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.