Kasar Isra'ila ta kama yaran Falasdin 562 ta kulle a kurkuku

Kasar Isra'ila ta kama yaran Falasdin 562 ta kulle a kurkuku

- A kwanakin bayane shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana birnin Kudus na kasar Isra'ila a matsayin helkwatar jakadancin Amurka

- Tun lokacin da shugaba Trump din ya bayyana wannan kudurin nashi sojojin Isra'ila suka kara kaimi wurin kama yara kanana na kasar Falasdin suna kullewa a kurkuku babu gaira babu dalili

Kasar Isra'ila ta kama yaran Falasdin 562 ta kulle a kurkuku
Kasar Isra'ila ta kama yaran Falasdin 562 ta kulle a kurkuku

Ba a jima ba bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana birnin Kudus a matsayin helkwatar jakadancin Amurka ta Isra'ila, sojojin kasar ta Isra'ila sun kara bada himma wurin kama yaran Falasdinawa.

DUBA WANNAN: Guguwar kankara ta jefa mutane milyan 70 cikin tashin hankali

Kafafen yada labarai sun bada rahoton cewa, bayan da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta cewar birnin Kudus shine zai zama helkwata na jakadancin Amurka a watannin da suka wuce, tun lokacin sojojin kasar ta Isra'ila suka kara kaimi wurin farautar Yara kanana na Falasdin, inda a yanzu haka sun kama yara sama da 562 basu ji ba basu gani ba.

An tabbatar da cewa, a yanzu haka sama da Falasdinawa 6,400 ne, inda sama da 300 daga cikin su yara ne kanana, aka kulle a gidajen kurkuku daban daban a kasar ta Isra'ila babu gaira babu dalili.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng