'Yan Adawan Isra'ila Sun Hadu za Su Kawo Karshen Mulkin Netanyahu
- Manyan 'yan jam'iyyun adawa a kasar Isra'ila sun hada kai domin kawo karshen mulkin Firaminisatan kasar, Benjamin Netanyahu
- Manyan 'yan adawar kasar Isra'ila, Naftali Bennett da Yair Lapid sun hada kai sun fitar da sanarwa da ke nuna cewa za su yi tafiya daya
- Benjamin Netanyahu na cigaba da fuskantar kalubale a siyasar Isra'ila tun bayan yakin da ya hada kai da Amurka ya kaddamar a Iran
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Isra'ila - Wasu manyan abokan hamayya guda biyu na Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, sun sanar da cewa sun hade karfi domin kifar da gwamnatin kawancen da yake jagoranta.
Manyan 'yan adawa a Isra'ila, Naftali Bennett da Yair Lapid sun fitar da sanarwa a ranar Lahadi suna bayyana hadewar jam’iyyunsu.

Source: Getty Images
'Yan adawa sun yi wa Netanyahu taron dangi
Rahoton Sky News ya nuna cewa Bennett ya ce za a kira sabuwar jam’iyyar da suka hada da suna Together, kuma shi ne zai jagorance ta.
Ya kara da cewa:
“Bayan shekaru 30, lokaci ya yi da za a rabu da Netanyahu kuma a bude sabon babi ga Isra’ila.”
Rahotanni sun nuna cewa sun ce za su fara wannan yunkuri ne a zaben da ake sa ran za a yi daga baya a wannan shekara.
Adawa ta kayar da Netanyahu a baya
Wadannan shugabannin biyu sun taba hada kai a baya, lokacin da suka kawo karshen mulkin Netanyahu na tsawon shekaru 12 a jere a zaben 2021.
Sai dai rahoton the Guardian ya nuna cewa sun kafa gwamnati ne ba tare da rinjaye mai yawa ba, wacce ta dauki kusan watanni 18 kacal.
Netanyahu, wanda shi ne firaminista mafi dadewa a Isra’ila, ya sake dawowa kan mulki bayan ya lashe zaben watan Nuwamba na 2022.

Source: Getty Images
Netanyahu zai iya faduwa zabe
Tun bayan yakin da aka fara, sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a sun nuna cewa yana iya faduwa a zaben da ake sa ran za a yi kafin karshen watan Oktoban 2026.
Bennett mai shekaru 54, tsohon soja kuma attajiri a fannin fasaha, yana biye da Netanyahu a sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a.
Wani bincike da aka fitar a Isra’ila a ranar 23 ga Afrilun 2026 ya nuna cewa Bennett na iya samun kujeru 21 cikin 120, yayin da jam’iyyar Likud ta Netanyahu ke kan kujeru 25.
Haka kuma binciken ya nuna jam’iyyar Lapid za ta samu kujeru bakwai kacal, kasa da kujeru 24 da take da su a halin yanzu.
Shugaban Israila ya yi wa Trump jaje
A wani labarin, mun kawo muku cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi magana kan harin da aka kai wa Donald Trump.
Ya bayyana cewa da shi da iyalan shi suna yi wa Trump barka da kubuta da ya yi tare da yaba wa jami'an tsaron Amurka bisa kare shi.
Wani matashi ne dauke da bindiga ya bude wuta yayin da Trump, mataimakin shi da manyan jami'an Amurka ke wani taro na musamman.
Asali: Legit.ng

