Firayim Ministan Isra’ila, Netanyahu Ya Bayyana a gaban Kotu a Tel Aviv a Karo na 88

Firayim Ministan Isra’ila, Netanyahu Ya Bayyana a gaban Kotu a Tel Aviv a Karo na 88

  • Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya sake gurfana a kotun Tel Aviv bayan zarge-zargen da ake yi masa wanda ya dauki tsawon lokaci
  • Netanyahu ya bayyana a gaban kotun karo har na 88 domin kare kansa daga tuhume-tuhumen rashawa da cin amanar ƙasa
  • Alƙalan kotun sun dawo da zaman shari’ar ranar Talata saboda dalilan tsaro da jadawalin siyasar Netanyahu, yayin da aka mayar da hankali kan wani zargi daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tel Aviv, Israel - Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya gurfana a gaban kotun yankin Tel Aviv ranar Talata 19 ga watan Mayun 2026.

Firayim ministan ya bayyana ne a gaban kotun domin amsa tuhume-tuhumen rashawa da ake yi masa tsawon lokaci.

Netanyahu ya bayyana a gaban kotu a Isra'ila
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu a birnin Tel Aviv. Hoto: Benjamin Netanyahu.
Source: Facebook

Netanyahu ya bayyana a gaban kotu

Wannan ne karo na 88 da Netanyahu ke bayyana a kotu tun bayan fara shari’arsa, wadda ta shafi zarge-zargen cin hanci da cin amanar ƙasa, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Duk da ƙaryata Amurka, an tabbatar da hannun Trump a hallaka jagoran ISIS a Najeriya

Majiyoyi suka ce alƙalai sun amince a dawo da zaman ranar Talata saboda matsalolin tsaro da jadawalin siyasa na Netanyahu.

Zaman ranar Talata ya mayar da hankali ne kan shari’ar 'Case 2000' bayan kammala tambayoyi a shari’o’in 'Case 1000' da 'Case 4000'.

Ana tuhumar Netanyahu da laifukan rashawa, karɓar cin hanci da kuma cin amanar ƙasa a cikin shari’o’i uku da aka buɗe tun 2019.

Sannan 'Case 1000' na zargin Netanyahu da iyalansa da karɓar kyaututtuka masu tsada daga attajirai domin samun wata irin tagomashi daga gwamnati.

A cikin 'Case 2000', ana zargin Netanyahu da tattaunawa da Arnon Mozes domin samun rahotannin da za su fifita shi a kafafen yaɗa labarai, cewar Anadolu Ajansi.

Ana zargin Netanyahu da cin hanci da cin amanar kasa
Firayim ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu yana jawabi a Tel Aviv. Hoto: Taylor Hill.
Source: Getty Images

Abin da Netanyahu ke cewa kan zarge-zargen

A bangaren 'Case 4000' kuwa na zargin Netanyahu da bai wa Shaul Elovitch wasu alfanu na gwamnati domin samun labarai masu kyau daga shafin Walla.

Tun bayan fara shari’ar a shekarar 2020, Benjamin Netanyahu ya ci gaba da musanta dukkan zarge-zargen, yana mai cewa makircin siyasa ne ake yi masa.

Kara karanta wannan

Trump ya nanata barazanar kawar da Iran daga doron kasa, ya fadi dalili

Dokar Isra’ila ta tanadi cewa shugaban ƙasa ba zai iya yi wa wanda ake tuhuma afuwa ba sai idan ya amsa laifin da ake zarginsa.

Baya ga wannan shari’a ta cikin gida, kotun hukunta manyan laifuka ta ICC na neman Netanyahu tun shekarar 2024 saboda laifukan yaƙi a Gaza.

Rahotanni sun ce sama da mutum 72,000 aka kashe a Gaza tun bayan fara yaƙin da aka shafe shekaru biyu ana yi tun Oktoban 2023.

Falasdinu: Isra'ila ta dura kan Lamine Yamal

Mun ba ku labarin cewa kasar Isra’ila ta yi martani mai zafi ganin ɗan wasan Barcelona ya daga tutar Falasdinu yayin murnar lashe gasar La-liga.

Abin da tauraron kulob din Barcelona ya yi ya jawo maganganunm yayin da wasu yabonsa duk da suka da ya ke sha a duniya.

Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya ce matakin dan wasan ya tayar da kiyayya, yayin da ake ci gaba da rikicin Gaza tsakanin Isra’ila da Hamas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.