2019: Jami'ar Cambridge ta kasar Ingila ta gayyaci 'yan takarar shugaban kasa 5

2019: Jami'ar Cambridge ta kasar Ingila ta gayyaci 'yan takarar shugaban kasa 5

Hukumar jami'ar Cambridge da hadin gwuiwar kungiyar daliban nahiyar Afrika dake karatu a makarantar (CUACS) sun kammala shirin gayyatar 'yan takarar kujerar shugaban kasa 5 daga Najeriya domin tattaunawa ta musamman dangane da zaben shekarar 2019.

Taron mai taken '2019 Nigerian Presidential Forum', za a gudanar da shi a watan Janairu na shekarar 2019.

A wata sanarwa da masu shirya taron suka fitar a jiya, Laraba, sun bayyana cewar tattaunawar zata bawa 'yan takarar damar ganawa da 'yan Najeriya dake kasar Ingila.

2019: Jami'ar Cambridge ta kasar Ingila ta gayyaci 'yan takarar shugaban kasa 5
2019: Jami'ar Cambridge ta kasar Ingila ta gayyaci 'yan takarar shugaban kasa 5
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Atiku ya fadawa CAN nufinsa ga Najeriya

Martine Dennis, dan jaridar kasar Ingila, ne zai zama mai gabatawa yayin tattaunawar.

"A yayin da Najeriya ke shirin yin zaben shugaban kasa a ranar 16 ga watan Fabrairu na shekarar 2019, wannan tattaunawar zata bawa 'yan takara damar bayyana manufofinsu ga Najeriya," a cewar sanarwar.

"Mun shirya gayyatar 'yan takara biyar; shugaba Muhammadu Buhari, Atiku Abubakar, Oby Ezekwesili, Kingsley Chiedu Moghalu, da Donald Duke, bisa la'akari da mukaman da suka rike a baya."

Wata kididdigar alkaluman daliban kasashen ketare dake karatu a kasar Ingila ta nuna cewar akwai a kalla 'yan Najeriya 20,000 dake karatu a jami'o'i daban-daban dake kasar Ingila.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel