Elon Musk Ya Siyar da Kadarorin da Ke Cikin Ofishin Twitter Domin Biyan Kudin Hayan da Ake Binsa

Elon Musk Ya Siyar da Kadarorin da Ke Cikin Ofishin Twitter Domin Biyan Kudin Hayan da Ake Binsa

  • Elon Musk ya yi amfani da wata dabara wajen warware bashin kudin haya da ake bin sabon kamfaninsa; Twitter
  • Kamfanin na Twitter na fama da matsalar kudin haya a ofishinsa na San Francisco watanni uku da siyarwa Musk
  • Musk ya yi gwanjon kayayyakin ofishin, ciki har da injunan hada kahwa, firij-firij, na’urori da injunan hada ‘pizza’ da sauransu

Elon Musk ya yi gwanjon wasu kayayyakin alatu da ke cikin kamfaninsa na Twitter domin ya biya kudin hawan da ake bin kamfanin, Washington Post ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne bayan da Musk, mai kamfanonin R=Tesla da SpaceX ya siya kamfanin Twitter a kan kudi $44m.

Musk dai ya dauki matakin rage kashe kudi a kamfanin Twitter saboda kamfanoni da yawa sun daina daura talla a kafar tasa.

Kara karanta wannan

Kamfen zub da jini: An sheke wani, da dama sun jikkata a kamfen PDP a wata jihar APC

Musk ya siyar da kayayyakin kamfanin Twitter
Elon Musk Ya Siyar da Kadarorin da Ke Cikin Ofishin Twitter Domin Biyan Kudin Hayan da Ake Binsa | Hoto: @elonmusk
Asali: Twitter

A cewar rahoton CNBC, kamfanin Heritage Global Partners ne ya gudanar da gwanjon, inda aka bajekolin na’urori da mutum-mutumin tambarin tsuntsuwar Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran kayayyakin da Musk ya yi gwanjonsu sun hada da tukwanen girki, firij-firij, injunan hada ‘pizza’ da kahwa da dai sauransu.

A ranar Litinin, 17 ga watan Janairu aka yi gwanjon kafcecen mutum-mutumin tambarin Twitter a kan kudi $17,500.

Wane ofishi ne aka yi gwanjon kayansa?

An yi gwanjon kayayyakin ne da suka hada kayan madafa, na’urori’ kayan girki da sauran abubuwan da ba lallai a amfana dasu ba a ofishin na San Francisco.

Idan baku manta ba, masu ginin ofishin Twitter sun maka kamfanin a kotu bisa gaza biyan kudin hayansa a kan kari.

An maka Twitter a kotu

Bayanan da aka gabatar a gaban kotun Califonia sun bayyana cewa, ana bin Twitter $136,260 na hayan ofishinsa da ke San Francisco.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Kama Kifi Mai Launin Ruwan Gwal, Ya Nemi Sanin Darajarsa Kafin Ya Cinye, Bidiyon Yadu

A baya, masu ginin sun ba Twitter wa’adin 16 ga watan Disamban 2022 domin warware bashin, lamarin bai samu saboda dalilai.

Musk dai ya so tattaunawa da masu ginin don sake rubuta yarjejeniyar haya ko mallakar wurin gaba daya ta hanyar siyar da wasu kayayyakinsa.

Elon Musk na ci gaba da jawo cece-kuce a kamfanin Twitter, a baya ya ce zai yi murabus daga mukamin shugaban kamfanin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel