Dalilin da Yasa ake Barazanar Rufe Facebook da Instagram a Najeriya
- Kamfanin Meta ya bayyana cewa yana iya rufe Facebook da Instagram a Najeriya saboda tarar makudan kudi da dokoki masu tsauri
- Najeriya ta kakaba wa Meta tara da ta kai Dala miliyan 290 bisa zargin karya dokoki daban-daban na kasuwanci da bayanan sirri
- Kamfanin Meta ta kasa kalubalantar wannan hukunci a kotun tarayya, inda aka ba shi wa’adi zuwa karshen Yuni don biyan tarar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kamfanin Meta, mai mallakar dandalin sada zumunta na Facebook da Instagram, ya yi barazanar rufe ayyukansa a Najeriya.
Meta ya yi barazanar ne bisa dalilin tarar da hukumomin kasar suka kakaba masa da kuma wasu sharuda da ya kira da sun fi karfinsa.

Asali: Getty Images
BBC ta rahoto cewa hukumar kare hakkin masu amfani da kayayyaki (FCCPC) da hukumar kula da bayanan sirri (NDPC) sun hada kai wajen kakabawa Meta tarar Dala miliyan 290 tun bara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meta ta shigar da kara a kotun tarayya da ke Abuja domin kalubalantar hukuncin, amma kotu ta yi watsi da karar, tare da ba kamfanin wa’adi zuwa karshen watan Yuni domin biyan tarar.
Meta ya yi barazanar rufe Facebook/Instagram
A takardar da ya shigar a kotu, Meta ya ce idan har aka tilasta masa bin sharudan hukumomin Najeriya, hakan na iya sa ya rufe Facebook da Instagram gaba daya a kasar.
Baya ga haka, Meta ya kara da cewa hukumar NDPC ta yi kuskuren fassara dokar kare bayanan sirri.
Hukumar NDPC ta bukaci Meta da ya nemi izini kafin ya tura bayanan masu amfani zuwa ga wasu, sharadin da Meta ya bayyana a matsayin "wanda ba zai yiwu ba."
Haka kuma, an bukaci kamfanin da ya samar da gajerun bidiyo na fadakarwa kan illolin da ke tattare da amfani da bayanan sirri ba da izini ba.

Asali: Getty Images
Rufe Facebook zai shafi tattalin 'yan Najeriya
Facebook na daya daga cikin manyan hanyoyin sadarwa da ‘yan Najeriya ke amfani da su a kullum wajen sadarwa da kuma gudanar da sana’o’in intanet.
Barazanar da Meta ta yi na iya haifar da cikas ga miliyoyin masu amfani da dandalin a Najeriya, musamman kananan ‘yan kasuwa da ke amfani da su a yau da kullum.
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa an nemi karin bayani daga Meta kan matakin da zai dauka na karshe, amma har yanzu ba a samu amsa ba daga kamfanin.
Yanzu dai lokaci na tafe domin ganin ko Meta zai bi sharudan Najeriya ko kuwa zai aiwatar da barazanar da ya yi.
Legit ta tattauna da Maryam Sulaiman
A wata hira da Legit ta yi da wata mai sayar da kaya a yanar gizo mai suna Maryam Sulaiman, ta bayyana cewa dakatar da Facebook zai shafi sana'ar ta.
Maryam ta ce:
"Muna rokon gwamnatin Najeriya da Meta su daidaita tsakaninsu. Ba ba za mu yi farin ciki da hakan ba saboda zai shafi sana'ar mu sosai."
Mai kamfanin Meta ya zama fitaccen mai kudi
A wani rahoton, kun ji cewa mai kamfanin Meta, Mark Zuckerberg ya shiga cikin sahun manyan masu kudin duniya.
A karkashin kamfanin Meta, Mark Zuckerberg ya mallaki kafofin Facebook, Instagram da Whatsapp da ake amfani da su wajen sada zumunta.
Mark Zuckerberg yana da mata 'yar asalin kasar China mai suna Priscilla Chan kuma Allah ya albarkaci auren su da 'ya'ya uku.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng