Buhari ya gwangwaje Afghanistan da tallafin $1m, OIC ta jinjina masa

Buhari ya gwangwaje Afghanistan da tallafin $1m, OIC ta jinjina masa

  • Kungiyar hadin kan Musulunci, OIC, taa mika godiyarta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan kyautar $1 miliyan da ya ba Afghanistan
  • Shugaban kungiyar, Hissein Brahim Taha, ya jinjinawa Najeriya kan gudunmawar da ta bai wa jama'ar Afghanistan domin walwalar dan Adam
  • Jama'ar Afghanistan sun fada cikin matsanancin halin yunwa da tsananin rayuwa, hakan yasa aka akafa gidauniyar tallafi ta Musulmai

Babban sakataran kungiyar hadin kan musulunci (OIC), Hissein Brahim Taha, yayi jinjina bisa yadda Najeriya ta bai wa kungiyar kula da walwalar dan adam ta Afghanistan "Kyautar dala miliyan daya".

A wata takarda da hedkwatar OIC ta tura wa Daily Nigerian, ta ce tallafin yazo daidai da lokacin kara wata sabuwar yarjejeniya ga kungiyar na kokarin ganin an kawo karshen halin da 'yan adam suka fuskanta a Afghanistan, don taimaka wa wajen biyan bukatun miliyoyin mutanen kasar, wadanda suka hada da mata da yara.

Kara karanta wannan

Jakadan Canada a Najeriya ya ziyarci marasa gata a kasan gada, hotunansu suna wasa sun taba zukata

Buhari ya gwangwaje Afghanistan da tallafin $1m, OIC ta jinjina masa
Buhari ya gwangwaje Afghanistan da tallafin $1m, OIC ta jinjina masa. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

OIC zata cigaba da mayar da hankali wajen nemo wa mutanen Afghanistan tallafi, sannan ba za tayi kasa a guiwa wajen kokari matuka don tabbatar da magance matsalar Afghanistan din a wata takarda da ministan kula da harkokin waje ya fitar a watan Disamba, 2021 a Islamabad, Jam'huriyar Pakistan ba.

"OIC tana rokon duk kasashe, masu mukamai da masu ruwa da tsaki da su zo su bada gudunmawar su ga kungiyar kula da walwalar bil adama ga Afghanistan ta asusun bankin daga cikin bankunan musuluncin da aka tanadar domin hakan (IsDB)," takardar ta kara da hakan.

OIC tayi kira ga kasashe da su bada nasu tallafin ga kungiyar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kungiyar tsakanin kasashen ta dakatar da biliyon dalolin na agaji da kadarori daga amfani, tun bayan da Taliban suka amshi mulkin kasar a watan Augustan 2021.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

Wannan raguwar da aka samu na tallafi da tsaida asusun bankin, ya jefa mutane cikin wani yanayi na bukatar taimakon gaggawa a Afghanistan, wanda hakan ya sanya miliyoyin mutane cikin tsananin yunwa da cutuka.

Dukiyar OIC da bankin musulunci ke kula da ita za ta fara taimakawa marasa karfi a farkon shekarar 2022.

OIC ta bayyana Najeriya a matsayin daya daga cikin kasashen da suka bada tallafi.

Kotun shari'a ta sa an jefe mace da namiji bayan an kama su dumu-dumu suna lalata

A wani labari na daban, an jefe wani mutum da wata mata a lardin arewa maso gabashin Badakhshan dake kasar Afghanistan, saboda sun aikata zina. Ma'aikatan Taliban ne suka tabbatar da hakan a ranar Laraba.

Wani ma'aikacin Taliban a lardin ya bayyana wa dpa yadda aka jefe su a kotun shari'a.

Shari'ar musulunci ba ta yarda musulmai maza da mata su sadu da juna in ba da aure ba.

Kara karanta wannan

Da-Dumi-Dumi: Lamari ya ɗau zafi, Ministan Buhari ya fice daga dakin taro da Daliban Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel