Babbar Magana: Amurka Ta Nemi Taimakon Majalisar Dinkin Duniya kan Iran
- Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya kara korafi game da kudurin da Amurka ta gabatar a Majalisar Ɗinkin Duniya kan Iran
- Kudirin na bukatar Iran ta dakatar da hare-hare da shimfiɗa bama-bamai a mashigar Hormuz domin hana jiragen da ta ki yarda da su wucewa
- Idan majalisar ta amince da kudurin, zai iya haifar da kakaba takunkumi kan Iran, har ma da ba da damar amfani da ƙarfi a kan Tehran
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Rahotanni sun nuna cewa kasar Amurka ta nemi agajin kasashen duniya da su amince da kudirin da ta gabatar a gaban majalisar dinkin duniya.
Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya sanar da cewa lokaci ya yi da kasashen duniya za su amince a dauki mataki kan toshe Hormuz da Iran ta yi.

Source: Getty Images
Legit ta tattaro bayanan da Macro Rubio ya yi ne a wani sako da ma'aikatar harkokin cikin gida ta Amurka ta wallafa a shafinta na X.
Korafin Amurka game da Iran
Rubio ya ce kudurin da Amurka ta gabatar zai gwada ko Majalisar Ɗinkin Duniya na da tasiri har yanzu, yana mai kira ga China da Rasha kada su sake hana shi wucewa.
Ya ce an yi wasu ƙananan gyare-gyare a harshen kudurin domin kauce masu hawa kujerar naki, amma bai tabbatar ko hakan zai yi tasiri ba.
Musayar wuta da aka yi a ranar Litinin ya nuna yadda rikicin ke cigaba, yayin da Amurka da Iran ke fafatawa kan iko da mashigar Hormuz mai muhimmanci ga makamashi da kasuwancin duniya.
A baya, wani kuduri da Bahrain ta gabatar tare da goyon bayan Amurka bai samu nasara ba bayan Rasha da China sun yi amfani da karfin da suke da shi a Majalisar Tsaro mai mambobi 15.
Sabon kudirin Amurka kan Iran
Sabon kudurin bai yi bayani kai tsaye ba game da ba da izinin amfani da ƙarfi, amma yana aiki ƙarƙashin Sashe na VII na majalisar, wanda ke ba Majalisar Tsaro damar ɗaukar matakai daga takunkumi har zuwa amfani da ƙarfi.
Reuters ta rahoto Rubio ya ce abin da suke nema kawai shi ne a yi Allah-wadai da Iran, a kuma bukace ta da ta daina kai hare-hare kan jiragen ruwa, ta cire bama-baman da aka shimfiɗa, tare da ba da damar kai agajin jin ƙai.
Ya kuma jaddada cewa yana da kyau China da Rasha su goyi bayan kudurin, domin hana rufe hanyoyin ruwa na duniya, musamman mashigin Hormuz, wanda zai iya jefa kasashe da dama cikin rikicin tattalin arziki.

Source: Getty Images
Ga bidiyon bayanin da Rubio ya yi:
Amurka: Iran ta gana da China
A wani labarin, mun kawo muku cewa ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya kai wata ziyara mai muhimmanci kasar China.
Abbas Araghchi ya yaba wa kasar China bisa yadda ta yi tsayuwar daka wajen adawa da Amurka kan hare-haren da Donald Trump ya kai Tehran.
A na shi bangaren, ministan harkokin wajen kasar China ya bayyana cewa suna tare da Iran kuma za su yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen yakin.
Asali: Legit.ng


