Sarki Charles III Ya Yi Bankwana da Duniya? Gaskiya Ta Bayyana

Sarki Charles III Ya Yi Bankwana da Duniya? Gaskiya Ta Bayyana

  • A ranar Litinin yanar gizo ta cika da zato da tsammanin samun 'babbar sanarwa' daga gidan sarautar Birtaniya
  • Rahotanni sun nuna cewa wasu kafafen yaɗa labarai sun bayyana cewa Sarki Charles III ya yi bankwana da duniya
  • Sai dai, kwatsam a ranar Talata, mai martaban ya bayyana wanda hakan ya kori jita-jitar cewa ya koma ga mahaliccinsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Londan, UK - Akwai jita-jitar da aka yi ta yaɗa wa ranar Litinin, 18 ga watan Maris 2024, cewa Sarkin Birtaniya, Charles III, ya mutu.

Sai dai, bayyanar da sarkin ya yi a bainar jama'a a ranar Talata, 19 ga watan Maris 2024, za ta kwantar da hankula sakamakon firgicin da aka shiga kan batun mutuwarsa.

Kara karanta wannan

Mutuwa rigar kowa: Fitaccen Furodusan fina-finai a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Sarki Charles III ya fito bainar jama'a
Sarki Charles III ya fito bainar jama'a yayin da ake jita-jitar mutuwarsa Hoto: Chris Johnson
Asali: Getty Images

Charles: Sarki yana nan da rai

Kamar yadda jaridar The News ta ruwaito a ranar Talata, 19 ga watan Maris, an ga Sarki Charles yana isa Clarence House a Westminster yayin da yake ci gaba da jinyar cutar daji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayyanar Sarkin dai ta kawo ƙarshen jita-jitar da aka yi ta yaɗa wa cewa numfashinsa ya ƙare a duniya.

Bayan ya kwashi lokaci kaɗan a Clarence House, an nuno shi yana ɗagawa mutane hannu, kafin daga bisani ya wuce birnin Landan.

Sarki Charles ya ci gaba da aikinsa

A yammacin ranar Talata, masarautar ta rubuta a shafin Twitter cewa Sarkin ya gana da tsoffin sojojin da suka fafata a yaƙin Koriya a fadar Buckingham don bikin cika shekaru 70 da sanya hannu kan yarjejeniyar da ta kawo ƙarshen yaƙin.

Kara karanta wannan

Zamfara: Sojojin Najeriya sun halaka wani shugaban ƴan bindiga da mayakansa

Wani ɓangare na rubutun na cewa:

"A safiyar yau Talata 19 ga watan Maris, Sarki ya gana da tsofaffin sojojin da suka fafata a yaƙin Koriya a fadar Buckingham domin bikin cika shekara 70 da rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta kawo ƙarshen rikicin.

An kwantar da Sarki Charles a asibiti

A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar Buckingham ta sanar da cewa an kwantar da Sarki Charles III a asibiti domin yi masa tiyata.

Sarkin wanda aka kwantar a wani asibitin kuɗi a birnin Landan, za a yi masa tiyatar mafitsara ne bayan ciwonsa ya ƙara tsananta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel