Dalilin da ya sa Croatia ta lallasa Najeriya – Kocin Najeriya

Dalilin da ya sa Croatia ta lallasa Najeriya – Kocin Najeriya

Babban kocin kungiyar kwallom kafa ta Super Eagles, Germot Rohr, ya sanar da cewa yawan tafka kura-kurai yayin da suke taka leda ne ya yi sanadiyan da kasar Croatia ta lallasa Najeriya da ci biyu.

Da ya ke bayani bayan kammala wasan ya ce ‘yan wasan Najeriya na hankalce da cewa sun yi kura-kurai a wasu muhimman lokutan da bai kamata su yi hakan ba.

Kocin na Najeriya ya ce gaba daya ‘yan wasan na sa sun yi jimamin yadda wasan ya karkare ba.

Dalilin da ya sa Croatia ta lallasa Najeriya – Kocin Najeriya
Dalilin da ya sa Croatia ta lallasa Najeriya – Kocin Najeriya

Rohr ya jaddada cewa kalubalen dake a gaban ‘yan Najeriya ya karu tunda kungiyar ta sha kashi.

KU KARANTA KUMA: Kaduna 2019: Zan kara da El-Rufai – Shehu Sani

Ya ce rawar da Mikel ya taka dama hakan suke so ya yi, kuma haka din ya ke yi tun farkon fra horas da ‘yan Najeriya da ya ke yi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku bide mu domin samun ingantattun labarai:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel