'Ban Adawa da Falasɗinu': Ɗan Majalisar Tarayya bayan Ganawa da Jakadan Isra'ila

'Ban Adawa da Falasɗinu': Ɗan Majalisar Tarayya bayan Ganawa da Jakadan Isra'ila

  • Dan majalisar tarayya ya yi karin haske kan zargin da ake yi masa cewa yana goyon bayan Isra'ila kan Falsɗinu
  • Hon. Wole Oke, ya karyata zargin cewa ganawarsa da jakadan Isra’ila na nufin adawa da kafa kasar Falasɗinu
  • Ya ce har yanzu yana goyon bayan tsarin da Najeriya ta dade tana bi don samun zaman lafiya tsakanin Isra’ila da Falasɗinu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban kwamitin harkokin ƙasashen waje na majalisar wakilai ya yi martani kan zargin fifita Isra'ila kan Falasɗinu.

Hon. Wole Oke, ya musanta rade-radin da ke cewa ya yi adawa da kafa Falasɗinu bayan ganawa da jakadan Isra'ila.

Dan majalisa ya karyata goyon bayan Isra'la kan Falasdinu
Dan majalisar tarayya daga Osun, Wole Oke. Hoto: House of Representatives.
Source: Facebook

Oke ya yi karin haske kan adawa da Falasdinu

Rahoton Vanguard ya ruwaito cewa dan majalisar ya fayyace ganawarsa da jakadan Isra’ila, Mista Michael Freeman domin wayarsa al'umma kai.

Kara karanta wannan

An jero sunayen tsofaffin gwamnoni 2 da ka iya maye gurbin minista a gwamnatin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Oke ya ce ganawar ba alamar goyon bayan Isra’ila ba ce, illa tattaunawa ta diflomasiyya tsakanin ƙasashe domin kawo ci gaba.

A cewarsa, Najeriya tana da matsaya ta dindindin na goyon bayan tsarin ƙasashen biyu da girmama doka don samar da zaman lafiya a yankin.

Ya bayyana a cikin wata sanarwa daga mataimakinsa, Tunji Iyanda, cewa rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta karya ne.

Hon. Wole Oke, wanda ke wakiltar mazabar Obokun/Oriade ta Osun, ya ce yana biyayya ga manufar Najeriya kan dangantakar ƙasashen duniya da zaman lafiya.

Ya kara da cewa tattaunawarsa da jakadan Isra’ila a Afrilun 2025 ta samo asali ne ta ofishin harkokin waje da hanyoyin majalisar, cewar rahoton Punch.

Dan majalisa ya musanta adawa da Falasdinu
Yan majalisar dokokin Najeriya yayin zama a Abuja. Hoto: House of Representatives.
Source: Facebook

Dalilin ganawar Hon. Oke da jakadan Isra'ila

Oke ya bayyana irin waɗannan ganawa da jakadu a matsayin al’ada ta diflomasiyyar majalisa, ba al’amuran sirri ko siyasa ba.

Ya nuna damuwarsa kan yadda wasu ke ɓata masa suna suna yada ƙarya da cewa ya sabawa matsayar Najeriya a harkokin waje.

Kara karanta wannan

Wasu daga cikin mutane 175 da Tinubu ya yi wa afuwa da laifin da suka aikata

Ya ce waɗannan bayanai na bogi ne da ke ƙoƙarin kawo masa cikas, yana mai cewa “babu gaskiya ko kaɗan cikin wannan magana.”

Oke ya jaddada cewa harkar manufofin kasashen waje na Najeriya ƙarƙashin ikon ma’aikatar harkokin ƙasashen waje ce, ba ta kowanne ɗan majalisa ba.

Ya kuma bayyana shirinsa na ganawa da jakadan Falasɗinu a Najeriya domin tabbatar da matsayin adalci da daidaito a dangantakar ƙasashe.

Najeriya dai ta sake nanata matsayarta na goyon bayan tsarin ƙasashen biyu a majalisar dinkin duniya a watan Satumba 2025 ta bakin mataimakin shugaban ƙasa.

Sulhu: Sheikh Gumi ya shawarci Falasdinawa

Kun ji cewa rahotanni sun tabbatar da cewa kowane bangare tsakanin Hamas da Isra'ila sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta domin samun zaman lafiya.

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, babban malami a Najeriya ya yi kira ga kungiyar Falasdinawa ta saki yahudawan da take tsare da su.

Malamin ya ce kungiyar Hamas na da hakki da hanyar kwato kasarta amma garkuwa da wasu fararen hula kuskure ne.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.