An Shiga Fargaba a Amurka, Wani Bature Ya Kamu da Cutar Hantavirus Mai Kisa
- An tabbatar da mutum daya daga cikin Amurkawa 17 da aka kwashe daga jirgin ruwan MV Hondius yana dauke da kwayar cutar Hantavirus
- Ana jigilar wadanda suka nuna alamun cutar a cikin wasu na'urori na musamman domin hana yaduwar cutar a cikin jirgin sama
- Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce nau'in kwayar cutar "Andes" tana da hadarin gaske, inda take iya kashe kashi 50 na wadanda ta kama
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Amurka - Ma'aikatar Lafiya ta Amurka (HHS) ta sanar da cewa an gano mutum daya yana dauke da kwayar cutar Hantavirus nau'in "Andes" a cikin Amurkawa 17 da ake kwasowa gida.
Wadannan mutane suna cikin wani jirgin ruwa na alfarma ne da cutar ta barke a cikinsa, kamar yadda HHS ta sanar a ranar Lahadi.

Source: Getty Images
Amurkawa sun kamu da cutar Hantavirus
Baya ga wanda aka tabbatar yana da cutar, akwai mutum na biyu da shi ma yake nuna wasu kananan alamu na rashin lafiya, masu alaka da Hantavirus, in ji rahoton Reuters.
Ma'aikatar HHS ta bayyana cewa:
"Yanzu haka an kwaso dukkan yan kasar Amurka ta jirgin sama, sannan an killace fasinjoji biyu da suka nuna alamun cutar a cikin na'urorin kariya ta musamman domin tabbatar da tsaro."
Cutar Hantavirus mai hadarin gaske
Kwayar cutar Hantavirus rukuni ne na kwayoyin cuta da yawanci beraye ke yada su, amma a wasu lokuta kalilan, tana iya yaduwa daga mutum zuwa mutum, in ji rahoton cibiyar CDC.
A yayin da cutar ta barke a wannan jirgi, an gano nau'in "Andes" wanda hukumar WHO ta ce tana haddasa mummunan ciwon fuka wanda ke iya kashe kusan rabin mutanen da ya kama.
Ya zuwa yanzu, mutane takwas ne suka fada cikin rashin lafiya a cikin jirgin na MV Hondius, inda aka tabbatar da shida daga cikinsu suna da kwayar cutar.

Source: Getty Images
CDC ta kwantar da hankalin jama'a
Tuni dai ma'aurata yan asalin kasar Holland da kuma wani dan kasar Jamus suka riga suka kwanta dama sakamakon wannan annoba.
Kasashe kamar Spain, Faransa, Kanada, da Birtaniya duk sun fara kwashe yan kasarsu daga jirgin wanda ke fake kusa da tsibirin Tenerife.
Wannan lamari ya janyo fargaba a sassan Amurka, inda mutane ke tsoron sake fada wa wata annobar irin ta baya, in ji rahoton Channels TV.
To sai dai Jay Bhattacharya, mukaddashin daraktan hukumar dakile cututtuka ta Amurka (CDC), ya bukaci jama'a da su kwantar da hankulansu, yana mai cewa Hantavirus ba ta kai hadarin COVID-19 ba.
Trump ya kamu da cutar CIV
A wani labari, mun taba ruwaito cewa, an gano shugaban Amurka yana dauke da cutar "Chronic Venous Insufficiency" bayan an yi gwaje-gwaje.
Mai magana da yawun Fadar White House, Karoline Leavitt, ta kira cutar CVI da "gama gari" inda jijiyoyin jini da suka lalace ke hana jini gudana yadda ya kamata.
Binciken ya zo ne bayan da Shugaba Donald Trump ya lura "ƙafafunsa ta wajen idon sahu sun fara kumbura" a cikin makonnin baya-bayan nan, in ji Leavitt.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

