Wani nau’in cutar COVID-19 mai mugun hadari da bai jin magani ya bulla a kasashen Afrika

Wani nau’in cutar COVID-19 mai mugun hadari da bai jin magani ya bulla a kasashen Afrika

  • Gwamnatin kasar Ingila ta tabbatar bullar wani sabon samfurin cutar COVID-19 mai suna B.1.1.529
  • Daga yau da rana, Birtaniya ba za ta sake karbar mutanen da suka fito daga yankin Afrika ta Kudu ba
  • Dokar za ta shafi fasinjoji daga Botswana, Lesotho, Eswatini, Zimbabwe da kuma kasar Namibiya

England - Gwamnatin Birtaniya ta sa takunkumin zuwa wasu kasashen Afrika a dalilin bullar sabuwar samfurin cutar COVID-19 a kasar Afrika ta Kudu.

Gwamnatin kasar ta tabbatar da wannan mataki da aka dauka ne a shafinta na yanar gizo bayan jami’an hukumar lafiya sun tabbatar da bullar wannan cuta.

Sanarwar tace gwamnati ta haramta tafiya da karbar wadanda suka fito daga kasashe Afrika ta Kudu, Botswana, Lesotho, Eswatini, Zimbabuwe da Namibiya.

Wannan takunkumi da aka sa zai fara aiki ne daga daren Ranar Juma’a, 26 ga watan Nuwamba, 2021.

Kara karanta wannan

N2.3tr muka ware don rabawa yan Najeriya kayan tallafin Korona, Gwamnatin tarayya

Jaridar Premium Times tace hakan yana nufin daga karfe 1:00 na ranar agogon Najeriya, ba za a karbi duk jirgin saman da ya fito daga wadannan kasashe ba.

Shin cutar ta shiga Ingila?

An gano wannan samufurin na kwayar Coronavirus ne a kasar Afrika ta Kudu a makon nan, kuma kawo yanzu ya hallaka mutane 59 a yankin da Hong Kong.

Wani nau’in cutar COVID-19
Ana jinyar masu COVID-19 Hoto: www.forbes.com
Asali: UGC

Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, har yanzu ba a samu mai dauke da wannan samfurin cutar a Birtaniya ba, amma an yi hakan ne domin a kare lafiyar al’umma.

Premium Times tace hukumar UKHSA na bincike a kan wannan sabon samfuri mai suna Variant B.1.1.529.

Hadarin sabon samfurin COVID-19?

Masana sun ce samfurin B.1.1.529 shi ne mafi hadari ga Bil Adama, a dalilin yadda cutar ta ke hayayyafa, kuma da alamun wannan nau’in ba ya jin magani.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta umarci dakatar da hakar man fetur a Bayelsa

“Alamun farko na nau’in cutar shi ne an fi saurin daukar shi kan samfurin Delta, kuma magungunan da ake da su ba su yi masa aiki sosai.” – Masani.

SARS-Cov-2 ya bulla a Delta

A tsakiyar shekarar nan ne aka ji hukumar NCDC ta tabbatar da cewa an gano sabon nau'in cutar Coronavirus mai suna SARS-Cov-2 a yankin Kudancin Najeriya.

A wancan lokaci kungiyar kiwon lafiya ta duniya watau WHO ta ce nau'in cutar COVID-19 da aka gano a jihar Delta za ta iya cigaba da yaduwa a jihohin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel