Mayakan Boko Haram Sun Kai Mummunan Hari Sansanin Sojoji, Dakaru 24 Sun Mutu a Chadi
- Wasu mahara da ake zargin mambobin Boko Haram ne sun kai hari kan sansanin sojin Chadi na Barka Tolorom da ke kusa da tafkin Chadi
- Harin na daren Litinin ya yi sanadiyyar mutuwar akalla sojoji 24, yayin da wasu majiyoyin tsaro suka bayyana cewa mutum 25 ne suka mutu
- Shugaba Mahamat Idriss Deby ya lashi takobin ci gaba da yaƙi da ƙungiyar Boko Haram har sai ya ga bayanta baki ɗaya a kasar Chadi
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Chadi - Ana zargin 'yan ta'addar Boko Haram masu ikirarin jihadi sun kai wani mummunan harin ba-zata a kan sansanin sojojin kasar Chadi.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan Boko Haram din sun kashe akalla dakarun sojojin Chadi 24 a wannan harin ba-zata.

Source: Getty Images
Boko Haram ta kashe sojojin Chadi 24

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun harbe babban malamin addinin Musulunci, ya mutu nan take a Pakistan
Jami'an soja da masu kula da yankin ne suka tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP wannan labari a ranar Talata.
Sansanin sojojin na Barka Tolorom yana gefen gaɓar tafkin Chadi ne, wanda ya raba iyaka tsakanin ƙasashen Kamaru, Chadi, Nijar, da Najeriya.
Tsibiran dake yankin sun daɗe suna zama mafaka ga mayakan Boko Haram da sauran ƙungiyoyin dake ikirarin jihadi.
Wata majiyar tsaro ta bayyana cewa harin da Boko Haram ta kai a daren Litinin ya yi sanadin mutuwar dakaru 25, yayin da wasu sojoji 46 suka sami raunuka.
Sai dai wani jami'in gudanarwa ya ce dakaru 24 ne kawai aka kashe, tare da jaddada cewa a yanzu haka komai ya lafa kuma jami'an tsaro sun dawo da iko da yankin.
Shugaban ƙasar Chadi ya yi martani
Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Deby Itno, ya yi Allah-wadai da harin ta shafinsa na Facebook a ranar Talata, inda ya bayyana shi a matsayin "aikin matsorata" da ƙungiyar Boko Haram ta aikata.
Ya miƙa saƙon ta'aziyya ga iyalan mamatan, tare da alƙawarin cewa ba za su dakata ba har sai an kawar da barazanar ta'addanci baki ɗaya.
Shugaba Mahamat Idriss Deby ya jaddada cewa:
"Za mu ci gaba da yaƙin nan tare da sabon karsashi har sai an kawar da wannan barazana baki ɗaya."

Source: Facebook
Kalubalen da ƙasar Chadi ke fuskanta
Ko da yake rundunar sojin ƙasar ta bayyana a watan Fabrairun 2025 cewa babu sauran mafakar Boko Haram a cikin ƙasar Chadi, yankin tafkin Chadi na ci gaba da fuskantar hare-hare, gami da garkuwa da mutane da ƙungiyar JAS ke yi.
Baya ga barazanar Boko Haram, yankin tafkin Chadi na zama mafaka ga ƙungiyar ISWAP, wadda ta ɓalle daga Boko Haram, kamar yadda Aljazeera ta ruwaito.
Kasar Chadi, duk da tana da arzikin man fetur, tana ci gaba da fuskantar matsalolin tattalin arziki, sauyin yanayi, da kuma tashe-tashen hankula na cikin gida waɗanda suka sa ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashe mafi talauci a Afirka.
An farmaki Fadar shugaban kasar Chadi
A wani labari, mun ruwaito cewa, wasu gungun ƴan ta'adda sun yi yunkurin kutsawa cikin fadar shugaban ƙasar Chadi a birnin N’Djamena amma ba su samu nasara ba.

Kara karanta wannan
Dakarun sojoji sun hallaka jagororin 'yan bindiga a Zamfara, an kashe 'yan ta'adda da dama
Dakarun rundunar sojojin ƙasar sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka yi masu luguden wuta kuma suka yi nasarar kashe wasu daga cikinsu.
Mutane sun fara zaman ɗar-ɗar a babban birnin bayan jin karar harbe-harbe a kusa da fadar mulki amma gwamnati ta ce an shawo kan lamarin.
Asali: Legit.ng
