Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban kasar Chadi, Mahamat Deby

Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban kasar Chadi, Mahamat Deby

Kun samu labarin cewa 'dan marigayi tsohon shugaban kasa, Idris Deby, ne aka zaba domin ya gajin mahaifinsa saboda shine shugaban majalisar sojojin kasar.

Ga wasu abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban Chadi:

1. Janar-Manjo Mahamat Deby Itno ya fara shiga makarantar Soja ne a kasar chadi

2. Daga baya ya samu horo a kasar Faransa, a makarantar Sojin Aix-en-Provence.

3. Bayan kammala a Faransa, an nada shi matsayin mataimakin kwamandan groupement infenterie.

4. Ya fita yakinsa na farko a Afrilun 2006 lokacin da yan tawaye suka kai hari babbar birnin kasar, daga baya kuma yayi musharaka a yaki a gabashin Chadi tare da Janar Abu Bakr Al Said.

Bayan yakin aka yi masa karin girma zuwa Manjo.

DUBA NAN: Ba za'a kara farashin man fetur ba a watan Mayu, Shugaban NNPC

Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban kasar Chadi, Mahamat Deby
Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban kasar Chadi, Mahamat Deby PHOTO: MARCO LONGARI / AFP
Asali: Twitter

DUBA NAN: Milyan 17 muka biya don a sake mana 'yayanmu 39 amma 10 aka saki, Iyayen daliban Kaduna

5. Ya jagoranci rundunar Sojojin kasar lokacin yakin Am Dam, inda dakarunsa suka ragargaji yan tawaye.

6. A Junairun 2013, an nada Mahamat matsayin mataimakin kwamandan rundunar Sojoji na musamman a Mali karkashin Janar Oumar Bikimo.

7. A ranar 22 ga Febrairu, ya jagoranci Sojoji wajen yakan yan tawaye a Adrar al-Ifoghas dake Arewacin Mali. Sun samu nasara a yakin amma sun yi rashin Sojoji 26.

8. Bayan yan tawayen FACT sun kashe mahaifinsa ranar 20 ga Afrilu, 2021, Sojoji sun zabesa matsayin shugaban rikon kwarya.

Mahamat Deby zai jagoranci kasar na tsawon watanni 18 yayinda majalisar Soji ke shirin gudanar da zabe.

Mun kawo muku rahoton cewa shugaban kasar Chadi, Idris Deby, ya riga mu gidan gaskiya, bayan samun nasara a zaben kasar.

Hukumar Sojin kasa ta ce Idris Deby ya mutu ne sakamakon harbin da akayi masa a faggen yaki da yan tawaye.

An saki sakamakon nasararsa a zaben ne ranar Litnin. Idris Deby ya mutu yana mai shekaru 68.

Ya hau mulkin kasar bayan tawaye a shekarar 1990. Ya lashe kashi 79.3% na zaben da aka gudanar ranar 11 ga Afrilu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel