Ana Batun Sake Zama, Shugaban Iran Ya Bayyana Abin da ba Za Su Yarda da Shi ba
- Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya sake yin tsokaci kan yakin da kasashen Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan kasarsa
- Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa hare-haren da aka kaddamar kan Iran sun saba wa dokokin kasa da kasa na duniya
- Shugaban Jamhuriyyar Musuluncin na Iran ya nuna cewa kasarsa ba za ta taba mika wuya ba ko sayar da 'yancin da take da shi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa babu babbar kasa a duniya da zai iya tursasa al’ummar Iran yin biyayya ko mika wuya.
Masoud Pezeshkian ya kuma soki irin salon "fuska biyu" da ake amfani da shi a siyasun ƙashen duniya.

Source: Twitter
Tashar Press tv ta kasar Iran ta ce Pezeshkian ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya yi a ranar Laraba, 15 ga Afrilu, 2026.
Shugaban Iran ya soki kasashen Yamma
Pezeshkian ya soki salon manufofin manyan ƙasashen duniya na yanzu, inda yake ishara ga ƙasashen Yamma, yana mai jaddada cewa duk wani harin soja da aka kai wa ƙasashe masu cin gashin kansu, ya sabawa ka'idojin da aka amince da su.
Wannan jawabi nasa, wanda ya yi shi yayin ziyarar rassa daban-daban na hukumar agajin gaggawa ta lardin Tehran, ya zo ne bayan da ƙungiyar sojin Amurka da Isra'ila suka ƙaddamar da yaƙi a kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu.
Hare-haren Amurka, Isra'ila sun yi barna
Hare-haren sun yi sanadiyyar kisan jagoran juyin juya halin Musulunci, Ayatollah Seyyed Ali Khamenei, da manyan kwamandojin soja, baya ga kisan ɗaruruwan farar hula, tashar IRNA ta kawo labarin.
Harin ya kuma shafi cibiyoyin tattalin arziƙi, gadoji, gidajen zama, makarantu, jami’o’i, asibitoci, da cibiyoyin ba da agaji na likitanci.
Shugaban na Iran ya nuna cewa babu dalilin da zai sanya a kai hare-hare kan kasarsa.

Source: Getty Images
Kasar Iran ba za ta mika wuya ba
“Wace hujja ce ta halatta harin soja a kan ƙasarmu? Wace hujja ce take akwai a cikin dokokin ƙashen duniya da ƙa’idojin jin ƙai na kai hari kan farar hula, ƙwararru, yara, da kuma ruguza muhimman cibiyoyi kamar makarantu da asibitoci?”
“Iran ba ta neman yaƙi ko rashin zaman lafiya, maimakon haka, koyaushe tana jaddada muhimmancin tattaunawa da mu’amala mai kyau da dukkan ƙasashen duniya."
"To sai dai, duk wani yunƙuri na ɗora wa ƙasar nan wani abu ko tilasta mata miƙa wuya ba zai yi nasara ba, kuma al’ummar Iran ba za su taɓa amincewa da wannan salon ba.”
- Masoud Pezeshkian
Jirgin Iran ya ratsa sojojin Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani babban jirgin dakon mai na Iran da ke ƙarƙashin takunkumi ya tsallaka mashigar ruwan Hormuz zuwa tashar Imam Khomeini duk da katangar da Amurka ta sanya.

Kara karanta wannan
Shugaba Putin ya kira takwaransa na Iran a waya, an ji abin da suka tattauna tsakaninsu
Jirgin dakon kayan na Iran wanda ke daukar kaya sosai, na iya ɗaukar gangunan danyen mai har miliyan biyu.
Bayanan bin diddigin jiragen ruwa, sun nuna cewa irgin da ke ɗauke da kayan abinci ya shiga Tekun Fasha kuma ya kama hanyarzuwa tashar Imam Khomeini ta Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

