'Yan Iran Sun Yi Watsi da Netanyahu, Sun Yi Zanga Zangar Goyon Bayan Khamenei
- Kasar Iran na cigaba da mayar da martani da makamai kan Isra’ila bayan harin da kasar Yahudawan ta fara kai mata a makon da ya gabata
- Dubban mutane sun yi zanga-zanga a Tehran, Iraq, Lebanon da Yemen suna nuna goyon baya ga gwamnatin Iran da Ayatollah Ali Khamenei
- A lokacin zanga zangar, an ji muryoyi na kira kan kin yarda da Isra’ila da Amurka, yayin da ake kara fargabar barkewar rikici a gaba ɗayan yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Yayin da rikicin tsakanin Isra’ila da Iran ke kara kamari, Iran ta harba makamai masu linzami a kan Isra’ila a matsayin martani ga harin da Tel Aviv.
Lamarin ya janyo gagarumar zanga-zanga a Tehran da wasu birane a Iran, inda dubban mutane suka fito suna nuna goyon baya ga jagoran juyin juya halin Iran, Ayatollah Ali Khamenei.

Asali: Getty Images
Al-Jazeera ta nuna yadda masu zanga-zanga suka rike hotunan manyan hafsoshin soja da suka rasa rayukansu tun bayan fara rikicin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga-zanga a Tehran da sauran biranen Iran
Yayin da ake cigaba da gwabza fada tsakanin Iran da Isra'ila, Farisawa sun fito titunan Tehran da wasu birane suna zanga zanga.
Tashar France 24 ta wallafa cewa wani mai shirya labarai a talabijin ya bayyana cewa:
“Wannan Juma’ar nuna haɗin kai ce da juriya daga al’ummar Iran.”
A cikin taron zanga zangar, an rubuta“zan ba da rayuwata saboda shugabana.” a jikin allon wani daga cikin masu zanga zangar
Hakanan an gudanar da zanga-zangar a biranen Tabriz a Arewa maso Yammacin Iran da Shiraz a Kudancin kasar, inda al’ummar Iran ke nuna goyon baya da ƙudurin ci gaba da fuskantar Isra’ila.
Limamin Juma’ar birnin Tehran, Mohammad Javad Haj Ali Akbari, ya bayyana cewa harin Isra’ila kan Iran alama ce ta “karaya” da “yunkurin tada hankalin jama’a su bijire wa gwamnati.”
Masu goyon bayan Iran sun fito a Iraq
A Iraq, dubban mabiyan fitaccen malamin Shi’a, Moqtada Sadr, sun gudanar da zanga-zanga a birnin Baghdad da wasu sassa na ƙasar.
Wani mai zanga-zanga, Abu Hussein, ya ce:
“Wannan yaki na zalunci ne... Isra’ila ba ta da hurumin kai hari.”
A garin Kufa kuma, masu zanga-zanga sun kona tutocin Isra’ila da Amurka domin nuna adawa da kasashen biyu.

Asali: Getty Images
An yi zanga zanga a Lebanon da Yemen
A Lebanon, daruruwan mabiyan Hezbollah sun gudanar da zanga-zanga a unguwannin Kudancin Beirut, inda suka daga tutocin Iran, Hezbollah da Lebanon.
An hango wasu masu zanga zangar rike da hoton Ayatollah Khamenei suna cewa wajibi ne su tsaya tare da Iran.
A birnin Sana'a na Yemen da wasu garuruwa, dubban mutane sun gudanar da gagarumar zanga-zangar nuna goyon baya ga Iran da adawa da Isra’ila da Amurka.
China ta ce Iran sun dade suna gwagwarmaya
A wani rahoton, kun ji cewa kasar China ta fito da wasu sharuda guda hudu da ta ce za su iya kawo karshen yakin Iran da Isra'ila.
Shugaban China ya ce zaman sulhu ne mafita a yakin ba wai kokarin nuna karfin soja ba kamar yadda Amurka ke nuna alamar yin hakan.
China ta kara da cewa Iran ta dade tana nuna tirjiya da jajircewa a tarihin duniya, wanda hakan ke nuna yadda taurin zuciya na 'yan kasar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng