Iran na Ci Gaba da Kai Hare Hare, Yahudawa Sun Fara Guduwa daga Gidajensu a Isra'ila
- Hare-haren da Iran ke ci gaba da kai wa ƙasar Isra'ila sun fara tilastawa yahudawa guduwa daga gidajensu domin tsira
- Rahotanni sun nuna cewa ƴan Isra'ila sun fara guduwa suna fakewa a tashohin jiragen ƙasa da ke ƙarƙashin ƙasa a yanzu
- Wannan na zuwa ne bayan Iran ta sake harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan Isra'ila a ranar Talata da ta gabata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Israel - Yahudawa da ake wa laƙabi da ƴan kama wuri zauna sun fara guduwa daga gidajensu a Isra'ila domin tsira da rayuwarsu.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan kasar Isra'ila sun fara zama ƴan gudun hijira a wurare daban-daban bayan sun baro gidajensu sakamakon hare-haren Isra'ila.

Asali: Getty Images
Wannan na zuwa ne awanni bayan ƙasar Iran ta ƙara tabbatar da cewa ta harba jerin makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan Isra'ila, rahoton CNN.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda yaƙi ya barke tsakanin Iran da Isra'ila
Tun farko dai Isra'ila ce ta fara kaddamar da hare-hare kan Iran, tana mai bayyana cewa ta ɗauki matakin ne domin lalata shirin ƙera makamin nukiliya.
Isra'ila ta kai hare-hare sau da dama kan sansanonin sojin Iran da wuraren ƙera nukiliya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar manyan hafsoshin sojin ƙasar ta musulunci.
Bayan waɗannan hare-hare, Iran ta mayar da martani ba tare da wani jinkiri ba, inda ta farmaki wurare masu muhimmanci a ƙasar ta Isra'ila.
Iran ta ci gaba da kai zafafan hare-hare kan Isra'ila, wanda a jiya Talata ƙasar ta tabbatar da cewa sabon farmakin da ta kai shi ne na 10 a jere.
Yahudawa sun fara guduwa daga gidajensu
Sai dai yayin da yaƙi tsakanin ƙasashen biyu ke ci gaba da tsananta, yahudawa mazauna Isra'ila sun fara barin gidajensu domin tsira daga hare-hare Iran.
A wani rahoto da Aminiya ta wallafa a shafin X, ta ce ƴan ƙasar Isra'ila sun fara guduwa suna neman mafaka a tashoshin jiragen kasa na karƙashin ƙasa.

Asali: Getty Images
Rahoton ya nuna cewa hare-haren da Iran ke ci gaba da kai wa sun hana su zama a gidajensu, hakan ya sa yahudawan suka fara gudu domin neman mafaka.
A yau Laraba, 18 ga watan Yuni, 2025 aka shiga rana ta shida da fara musayar wuta tsakanin Iran da Isra'ila, ƙasashen da suka jima suna takun-saƙa a tsakaninsu.
Iran ta ƙara samun nasara kan Isra'ila
A wani rahoton, kun ji cewa ƙasar Iran ta lalata muhimman wurare a matatar man Isra'ila da ke Haifa, lamarin da ya tilasta dakatar da aiki nan take.
Iran ta samu wannan nasara ne biyo bayan hare-hare da ta kai da rokoki kan biranen Isra'ila yayin da yaƙi ke kara tsananta tsakanin kasashen guda biyu.
Kamfanin Bazan Group, wanda ke kula da matatar, ya bayyana cewa harin ya tilasta musu rufe ayyuka gaba ɗaya, yayin da rikicin ke kara zafi tsakanin Isra’ila da Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng