A Karshe, Majalisar Dinkin Duniya Ta Tsoma Baki kan Rikicin Iran da Isra'ila

A Karshe, Majalisar Dinkin Duniya Ta Tsoma Baki kan Rikicin Iran da Isra'ila

  • Hukumar kare hakkin bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta nemi a gaggauta kawo karshen rikicin Iran da Isra’ila da tattaunawar diflomasiyya
  • Hukumar ta ce ya zama dole a kare fararen hula yayin da hare-haren makamai ke cigaba da halaka mutane a birane
  • Jakadan Iran ya ce hare-haren Isra’ila kan gine-ginen nukiliya barazana ne ga lafiyar jama'a, yana kira da a hukunta kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

New York, Amurka - Yayin da rikicin Iran da Isra’ila ya shiga rana ta shida, Majalisar Dinkin Duniya ta yi magana.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce abin takaici ne har yanzu ana cigaba da kai ruwa rana wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi.

Majalisar Dinkin Duniya ta magantu kan rigimar Iran, Isra'ila
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci tsagaita wuta a rikicin Iran da Isra'ila. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Iran/Isra'ila: Majalisar Dinkin Duniya ta magantu

Jami'ar kula da ofishin kare hakkin dan Adam, Nada Al-Nashif ita ta tabbatar da haka kamar yadda shafin Majalisar ya wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Al-Nashif ta bukaci a gaggauta kawo karshen harin makamai da ake yi kusan mako guda kenan tsakanin Iran da Isra'ila.

Isra’ila ta fara kai hari kan sansanonin nukiliya da na soja a fadin Iran tun ranar Juma’a, inda Iran ta mayar da martani kan biranen kasar.

“Ofishin kare hakkin bil’adama na MDD yana kira da a sassauta rikicin da kuma gudanar da tattaunawar diflomasiyya domin kawo mafita.
“Muna bibiyar lamarin sannan muna da rahotanni cewa dubban mutane suna tserewa daga wasu sassan Tehran saboda gargadi da aka bayar."

- Cewar Al-Nashif

An buƙaci tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci tattaunawa kan rigimar Isra'ila da Iran. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

Majalisar ta nuna damuwa da kisan fararen hula

Rahotanni na baya-bayan nan daga yankin sun nuna cewa sama da mutane 200 sun mutu a Iran yayin da 24 suka mutu a Isra’ila.

Al-Nashif ta shaidawa taron Majalisar Kare Hakkin Bil’adama a Geneva cewa akwai damuwa matuka ganin yadda harin ya shafi wuraren da mutane ke da yawa.

Ta ce:

“Ya zama wajibi bangarorin biyu su mutunta dokar kasa da kasa ta kare fararen hula da dukiyarsu a wuraren da jama’a ke da yawa.
“Muna kira ga duk masu tasiri su shiga tattaunawa cikin gaggawa."

- Cewar hukumar

Jakadan Iran, Ali Bahreini, ya bayyana harin Isra’ila da cewa shine mafi muni da ya faru tun 13 ga Yuni, yana kira da a hukunta Isra’ila.

Ya zargi Isra’ila da kai hare-haren kauyuka da barazana ga kayan amfanin jama’a, ciki har da ruwan sha da kuma gine-ginen nukiliya da ke birnin Tehran.

'Yan Israila sun fara tserewa daga gidajensu

Kun ji cewa a cigaba da kai hare-haren da Iran ke kai wa ƙasar Isra'ila, Yahudawa sun fara guduwa daga gidajensu.

Majiyoyi sun nuna cewa ƴan Isra'ila sun fara guduwa suna fakewa a tashohin jiragen ƙasa da ke ƙarƙashin ƙasa a halin da ake ciki yanzu.

Hakan ya biyo bayan sake harba makamai masu linzami da Iran ta yi da jirage marasa matuka kan Isra'ila a ranar Talata da ta gabata.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.