Amurka Za Ta Ƙaƙaba Takunkumi kan Najeriya da Sauran Ƙasashen Afirka 24

Amurka Za Ta Ƙaƙaba Takunkumi kan Najeriya da Sauran Ƙasashen Afirka 24

  • Gwamnatin Donald Trump na duba yiwuwar sanya takunkumin biza ga Najeriya da wasu ƙasashe 24 na Afirka
  • Wasikar da Marco Rubio ya sa wa hannu ta ce wasu ƙasashen sun kasa bayar da ingantattun takardu ko hana ‘yan ƙasa yin tartsatsi da biza
  • Kungiyar Tarayyar Afirka ta gargadi Amurka cewa irin waɗannan matakai masu tsauri za su iya lalata dangantakarsu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Gwamnatin Amurka ƙarƙashin Donald Trump na shirin sanya takunkumin biza kan Najeriya da ƙasashe 24 na Afirka

Gwamnatin Amurka na duba yiwuwar ƙara takunkumin biza ne saboda dalilai na kin bin ka'idojin tsaro.

Amurka za ta ƙaƙaba takunkumi ga Najeriya
Amurka za ta ƙaƙaba takunkumi kan Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Donald Trump.
Asali: Getty Images

Jerin kasashen da Amurka za ta ƙakabawa takunkumi

Rahoton Washington Post ya bayyana cewa sakataren harkokin waje Marco Rubio ne ya sa wa wasikar hannu, inda aka aika da ita ga jakadu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin jerin sunayen akwai ƙasashe irin su Angola, Ghana, Kamaru, Sudan ta Kudu, Misira da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

Gwamnatin Amurka ta ce ƙasashen sun kasa samar da takardun shaida masu inganci kuma ana zargin su da damfara da kuma yawan tartsatsi da biza.

Wasu kuma ana zargin suna ba da zama na ƙasa ga masu kudi ba tare da zama a ƙasar ba, har da kalaman kin Amurka.

Sai dai Amurka ta ce ƙasashen da suka amince da karɓar ‘yan gudun hijira ko rattaba hannu kan yarjejeniyar za su tsira.

An ba ƙasashen da abin ya shafa wa’adin kwana 60 su cika sharuɗɗan da aka shimfiɗa, su kuma mika shirin farko kafin Laraba da safe.

An shirya ƙaƙaba takunkumi kan Najeriya a Amurka
Amurka ta shirya ƙaƙaba takunkumi kan Najeriya da wasu ƙasashe 24. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Martanin kungiyar AU kan takunkumi

A baya dai, Kungiyar Tarayyar Afirka ta ce irin waɗannan matakai marasa tushe na iya gurgunta dangantaka da Amurka mai tsawon shekaru, cewar Premium Times.

Kungiyar ta bukaci gwamnatin Amurka da ta rungumi matakai na adalci da suka dogara da hujja wajen yanke hukunci kan harkokin shige da fice.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta ce:

"Ta na ci gaba da nuna damuwa kan illolin da irin waɗannan matakai za su iya haifarwa ga hulɗar mutane da mutane, musayar ilimi, kasuwanci, da kuma alakar diflomasiyya da aka gina tsawon shekaru.”

AU, wacce ke wakiltar duk ƙasashe 55 na nahiyar Afirka, ta roƙi gwamnatin Washington da ta ɗauki hanyar tuntuba da shawarwari tare da shiga cikin tattaunawa.

Ta ce hakan zai zama mai amfani da ƙasashen da abin ya shafa,” tare da yin kira ga “bayyananniyar sadarwa” domin magance matsalolin da ke ƙasa.

Trump ya hana wasu ƙasashe shiga Amurka

Kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump ya sanya hannu kan dokar hana mutane daga ƙasashe 12 shiga ƙasar, ciki har da Iran.

Donald Trump ya bayyana cewa matakin zai kare Amurkawa daga “mutane masu haɗari” da ke fitowa daga kasashe ƙetare.

Haramcin zai fara aiki daga ranar 9 ga Yuni, 2025, kuma yana ɗaya daga cikin alkawuran yaƙin neman zaɓensa na 2024

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.