'Dillacin Kwayoyi': Amurka Ta Fadi Lokacin Fitar da Bayanan Sirri game da Tinubu
- FBI da DEA sun nemi karin kwanaki 90 domin fitar da kan zargin shari’ar safarar kwayoyi da ake alakanta ta da Shugaba Bola Tinubu
- Dan gwagwarmaya, Aaron Greenspan ya ki amincewa da bukatar hukumomin, inda ya nemi su takaita lokacin zuwa kwanaki 14 kacal
- Kotun Koli ta Kasa da ke Amurka ta umurci hukumomin da su gaggauta fitar da takardun bincikensu da ba su keɓantu da FOIA ba kafin yau
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - Hukumomin FBI tare da DEA da ke Amurka sun nemi ƙarin kwanaki 90 don kammala gabatar da rahotannin bincike da suka shafi zargin shari’ar kwayoyi da ake alakanta da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda da aka shigar da ita a gaban Kotun Ƙoli ta Ƙasa da ke Columbia, kasar Amurka a ranar Alhamis.

Asali: Twitter
An tafka muhawara a kotun Amurka
Shari’ar ta shafi zargin da ake cewa Tinubu yana da hannu a wata kungiyar safarar miyagun kwayoyi a birnin Chicago tun a shekarun 1990, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai wanda ya shigar da karar, Aaron Greenspan, ɗan gwagwarmaya kan kare gaskiya da adalci a Amurka ya yi adawa da bukatar FBI da DEA.
Aaron Greenspan, wanda ya kafa dandalin PlainSite, ya yi watsi da bukatar karin kwanaki 90 da suka nema, yana mai ba da shawarar a takaita lokacin zuwa kwanaki 14.
Yadda shari'ar binciken 'su Tinubu' ta gudana
Tun da farko, alkalin kotun, Mai Shari’a Beryl Howell, ta umarci FBI da DEA da su ba da rahoton ci gaban bincike tare da sakin duk wata takarda da ba ta keɓanta daga FOIA ba kafin ranar 2 ga Mayu, 2025.
Aaron Greenspan ya shigar da buƙatu 12 karkashin dokar FOIA tsakanin shekarar 2022 zuwa 2023, yana neman bayanai kan wata ƙungiyar safarar kwayoyi da ke da alaƙa da Chicago, inda ake zargin wasu mutane hudu ciki har da Tinubu ke tafiyar da ita.
A baya, FBI da DEA sun fitar da rahoton kin tabbatarwa ko ƙaryata kasancewar irin waɗannan bayanai, amma kotu ta yanke hukunci cewa wannan martani bai dace da wannan shari’a ba.
A cikin rahoton matsayar hadin gwiwa da aka gabatar a ranar 1 ga Mayu, 2025, FBI da DEA sun sanar da kotu cewa suna bukatar karin lokaci don kammala bincikensu.

Asali: Getty Images
FBI, DEA sun nemi karin kwanaki 90
Jaridar Punch ta rahoto Greenspan ya ce ya kamata hukumomin su mika takardun da suka riga suka gano ba tare da cire wani ɓangare ba, kafin mako mai zuwa.
Rahoton ya ce:
“Wadanda ake ka FBI da DEA sun ba da shawarar a dage gabatar da rahoton zuwa ko kafin 31 ga Yuli, 2025, domin sanar da kotu halin da ake ciki bayan kammala bincike.
"Sai dai wanda ya shigar da karar ya na ganin wannan wa'adi da FBI da DEA suka nema ya yi tsayi, inda ya nemi a fitar da rahoton 31 ga Mayu, 2025.”
Tinubu ya yi yunkurin hana binciken FBI
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya yi ƙoƙarin hana hukumomi shida na Amurka sakin wani tsohon rahoto da ke da nasaba da zargin da ake masa.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumomi irin su FBI na shirin fitar da cikakken bayani kan wata shari’a da ta shafi safarar miyagun ƙwayoyi da aka ce Tinubu na da alaƙa da ita tun 1993.
A wancan lokaci, Tinubu ya sallama $460,000 da ke hannunsa, bayan bincike kan wata ƙungiyar da ake zargin yana da hannu a harkar safarar ƙwayoyi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng