Congo: An Shiga Fargaba Yayin da Aka Yi Yunkurin Juyin Mulki, an Yaɗa Bidiyon

Congo: An Shiga Fargaba Yayin da Aka Yi Yunkurin Juyin Mulki, an Yaɗa Bidiyon

  • Sojojin Dimukradiyyar Congo sun dakile wani mummunan hari na juyin mulki a yau Lahadi 19 ga watan Mayu a kasar
  • Kakakin rundunar a kasar, Sylvain Ekenge shi ya tabbatar da haka inda ya ce an yi nasara kan abokan gaba
  • Ekenge ya bayyana cewa daga cikin wadanda aka kama da zargin kawo harin har da mayakan ketare da kuma wasu ƴan kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kinshasa, DR Congo - Rundunar sojojin Dimukradiyyar Congo sun tabbatar da cewa sun yi nasarar dakile juyin mulki a ƙasar.

Dakarun suka ce ƴan Congo da wasu mayaƙa daga ketare ne suka kawo harin wanda aka dakile a yau Lahadi 19 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

A karon farko, an yi bikin nuna ado a Saudiyya da mata suka fitar da cinyoyinsu waje

An dakile yunkurin juyin mulki a Congo
An cafke wasu da yunkurin juyin mulki a Congo. Hoto: Glody Murhabazi.
Asali: Getty Images

Rundunar sojojin Congo ta yi martani

Kakakin rundunar a kasar, Sylvain Ekenge shi ya tabbatar da haka yayin wani jawabi a gidan talabijin na kasar, RTNC TV, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun yi nasarar dakile harin juyin mulki da ƴan Condo da wasu mayakan ketare suka kawo."
"An yi nasarar cafke mutane da dama da ake zargi, yanzu komai ya daidaita babu wata matsala."

- Sylvain Ekenge

Sai dai Ekenge bai ba da cikakken bayani kan lamarin ba wanda ya ta da hankulan mutane.

Wannan shi ne karo na biyu a cikin shekara daya da ake yi kun juyin mulki a kasar.

An yi yunkurin juyin mulki 2 a shekara

A watan Faburairun 2022, shugaban kasar, Felix Tshisekedi ya sanar da yunkurin juyin mulki a kasar yayin da yake halartar ganawa da kungiyar AU.

Hakan shi ya tilasta Tshisekedi barin ganawar wanda shi ne shugaban kungiyar domin dakile matsalar cikin gida a kasarsa.

Kara karanta wannan

An kame satasan da suka yi amfani da bindigar sasan yara wajen Sace mota a Enugu

Bidiyo da hotunan halin da ake ciki:

Gwamnatin ta yi magana kan jita-jitar juyin mulki

A wani labarin, Gwamnatin kasar Congo ta musanta rahotannin yunkurin juyin mulkin da aka yi wa shugaba Felix Tshisekedi na kasar wanda ya shafe shekaru 38 yana mulki.

Wannan na zuwa ne a bayanin Ministan Yada Labarai na Kongo Thierry Moungalla wanda ya wallafa abin da ke faruwa a shafinsa na Twitter.

An yi ta samun juyin mulki a fadin Afirka inda a baya-bayan nan aka yi a Gabon da kuma Nijar, inda aka hambarar da shugabannin kasashen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.