Rikici: Da Gaske Ne An Yi Yunƙurin Juyin Mulki a Kasar Saliyo? Karin Bayani

Rikici: Da Gaske Ne An Yi Yunƙurin Juyin Mulki a Kasar Saliyo? Karin Bayani

  • Labari ya bazu cewa an yi yunƙurin juyin mulki a ƙasar Saliyo, yayin da ECOWAS ke tattauna batun juyin mulkin Nijar
  • An samu fargaba a ƙasar ta Saliyo biyo bayan sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da ya gudana a watan Yuni
  • Jami'an 'yan sandan ƙasar sun tabbatar da kama wasu sojoji da wasu jami'an 'yan sanda dangane da batun

Freetown, Sierra Leone - Saliyo ƙasa ce a Afrika ta Yamma da aka yaɗa labarin yunƙurin juyin mulkin da aka ce sojoji da 'yan sanda sun so su yi a cikinta a kwanakin baya.

Labarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake tattake wuri kan juyin mulkin da sojoji suka gudanar a jamhuriyyar Nijar.

An yi yunkurin yin juyin mulki a ƙasar Sierra Leone
An shiga fargaba saboda yunƙurin juyin mulki a ƙasar Saliyo. Hoto: Julius Maada Bio, Samura Kamara
Asali: Facebook

Rikicin siyasar ƙasar Saliyo

Rahoton da VOA Africa ta yi ya nuna cewa 'yan ƙasar ta Saliyo sun shiga fargaba biyo bayan saɓanin da aka samu tsakanin 'yan adawa da kuma gwamnatin da ke riƙe da madafun iko.

Kara karanta wannan

Shugaban 'Yan Bindiga Ya Ayyana Kansa a Matsayin Gwamnan Jihar Arewa? Gaskiya Ta Bayyana

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A watan Yunin shekarar 2023 ne dai aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Saliyo, inda Shugaba Julius Maada Bio ya sake lashe zaɓen a karo na biyu kamar yadda Aljazeera ta kawo rahoto.

Sai dai babban abokin gamayyar Julius Maada wato Samura Kamara na jam'iyyar APC, ya yi watsi da sakamakon zaɓen wanda bayan nan ne kuma aka yaɗa jita-jitar cewa ana yunƙurin kifar da gwamnatin ƙasar.

'Yan sanda sun kama jami'ansu, sojoji da fararen hula a Saliyo

Biyo bayan jita-jitar juyin mulkin ne rundunar 'yan sandan ƙasar ta Saliyo suka gabatar da kame na wasu daga cikin sojoji, 'yan sanda, da ma fararen hula da ake zargi da hannu a ciki.

Mataimakin Sufeto Janar na 'yan sandan ƙasar ta Saliyo Brima Jah, ya bayyana cewa sun kama mutanen ne saboda zarginsu da yunƙurin tayar da hankalin 'yan ƙasa da aka yi.

Kara karanta wannan

Rikicin Nijar: An Fara Fuskantar Karancin Shanu Da Tumaki Bayan Rufe Iyakoki

Sai dai wani rahoto na Africa News ya ce, har yanzu ba a san adadin mutanen da aka kama dangane da zargin juyin mulkin na ƙasar Saliyo ba.

Tchiani ya soki takunkumin da ECOWAS ta ƙaƙabawa Nijar

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan sukar da shugaban mulkin soji na jamhuriyar Nijar, Abdourahmane Tchiani ya yi wa takunkumin da ƙungiyar ECOWAS ta sanyawa ƙasar sa.

Ya bukaci ECOWAS ta janye takunkumanta da ya kira na rashin adalci, domin kuwa suna wahalar da al'ummar jamhuriyar Nijar.

Ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar a akwatin gidan talabijin na ƙasar a makon da ya gabata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng