Juyin Mulki: Halin da Ake ciki a Cote d'Ivoire kan Batun Hambarar da Alassane Ouattara
- An yi ta yaɗa jita-jitar cewa dakarun sojoji sun hamɓarar da gwamnatin Shugaba Alassane Ouattara na ƙasar Cote d'Ivoire
- Ana cikin yaɗa jita-jitar sai fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa Alassane Ouattara ya halarci wani muhimmin taro
- Jita-jita kan juyin mulkin dai ta bazu a shafukan sada zumunts, aka cewa har babban hafsan sojojin ƙasar aka kashe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Birnin Abidjan - Shugaban ƙasar Côte d’Ivoire, Alassane Ouattara, ya jagoranci taron majalisar ministoci a ranar Laraba.
Taron ya gudana a fadar shugaban ƙasa da ke birnin Abidjan, babban birnin ƙasar, yayin da ake jita-jitar sojoji sun yi juyin mulki.

Asali: Facebook
Fadar shugaban ƙasar ta tabbatar da halartar Alassane Ouattara a taron cikin wata sanarwa da ta fitar a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kuma sanya hotunan da ke nuna shugaban ƙasa da ministocinsa suna halartar zaman.
Daga cikin batutuwan da aka tattauna a taron akwai buƙatar faɗaɗa hanyoyin samar da wutar lantarki da kuma samar da gidaje masu inganci ga ƴan ƙasa.
An yaɗa jita-jitar hamɓarar da Alassane Ouattara
Taron ya gudana ne a daidai lokacin da ake yaɗa jita-jitar juyin mulki a shafukan sada zumunta na ƙasar.
Waɗannan jita-jita sun bazu ta shafuka da dama na sada zumunta irin su X, Facebook, TikTok, da ma wasu gidajen yada labarai na gargajiya.
Har ila yau, jita-jitar ta shafi Lassina Doumbia, babban hafsan hafsoshin sojojin ƙasar, inda wasu ke cewa shi ma an kashe shi.

Asali: Facebook
Menene gaskiya kan juyin mulki a Cote d'Ivoire?
TheCable ta tuntubi wasu ƴan jarida a Côte d’Ivoire domin tabbatar da sahihancin jita-jitar. Sun musanta rahotannin, suna masu cewa babu gaskiya a ciki.
Christelle Kouamé ƴar jarida da ke zaune a birnin Abidjan ta bayyana cewa ana zaune cikin kwanciyar hankali.
Ta kuma musanta cewa an katse intanet a ƙasar sakamakon jita-jitar juyin mulkin da ake yaɗawa.
Christelle Kouamé na cikin kwamitin zartarwa na ƙungiyar ƴan jarida ta ƙasa da kuma mamba a ƙungiyar ƴan jarida masu bincike ta Côte d’Ivoire.
“Babu wani juyin mulki a Côte d’Ivoire. Ƙasar tana cikin kwanciyar hankali."
“Shugaban ƙasa ya halarci bikin buɗe taron Africa CEO Forum a makon da ya gabata. A yau ma, ya halarci taron majalisar ministoci."
“Labaran ƙarya ne kawai. Mutane na amfani da intanet yadda suke so. Amma da intanet ɗin ne nake magana da ku yanzu."
- Christelle Kouamé
Yawan yaɗuwar jita-jitar juyin mulki a ƙasashen Yammacin Afirka yana ƙara ƙaruwa, lamarin da ke nuna yadda yankin ke fama da rashin tabbas a siyasa, raunana tsarin dimokuraɗiyya, da kuma ƙarancin amincewa da gwamnatocin farar hula.
An yi yunƙurin juyin mulki a kasar Congo
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu sojoji sun yi yunƙurin hamɓarar da gwamnatin farar hula a ƙasar Dimokuraɗiyyar Congo.
Rundunar sojojin ƙasar ta tabbatar da cewa ta samu nasarar daƙile yunƙurin juyin mulkin da aka yi.
Bayan daƙile yunƙurin juyin mulkin, rundunar ta bayyana cewa wasu ƴan ƙasar ne da kuma ƴan ƙasashen ƙetare suka kawo harin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng