An Shiga Fargabar Juyin Mulki a Makwabciyar Najeriya Yayin da Aka Yi Harbe-Harbe, Bidiyom Ya Bayyana

An Shiga Fargabar Juyin Mulki a Makwabciyar Najeriya Yayin da Aka Yi Harbe-Harbe, Bidiyom Ya Bayyana

  • An kashe Yaya Djerou Dillo, shugaban jam'iyyar adawa ta Socialist Party Without Borders (PSF) ta ƙasar Chadi mai makwabtaka da Najeriya
  • An kawar da Dillo ne a ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairun 2024, a lokacin musayar wuta da jami’an tsaro
  • Legit Hausa ta fahimci cewa Yaya Dillo mai shekaru 49 a duniya, ɗan uwan ​​shugaban riƙon ƙwarya na ƙasar ne, Mahamat Idriss Deby Itno

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

N'Djamena, Chadi - An kashe Yaya Dillo, madugun ƴan adawa a ƙasar Chadi a yayin wani artabu da jami'an tsaro.

Kamar yadda BBC ta ruwaito a ranar Alhamis, 29 ga Fabrairu, jami’ai sun tabbatar da mutuwar Dillo.

An halaka yaya Dillo
Yaya Dillo ya rasa ransa yayin musayar wuta da sojoji Hoto: @honore123
Asali: Twitter

Mutuwar Yaya Dillo na zuwa ne bayan da gwamnatin ƙasar ta dora alhakin harin da aka kai kan hukumar leƙen asirin ƙasar. Zargin da Dillo ya musanta.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP zai ba 'yan adawa mukamai masu gwabi a jiharsa, ya fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Legit Hausa ta fahimci cewa ana sa ran Dillo zai tsaya takara a zaɓen shugabam ƙasa da za a gudanar a watan Mayun 2024.

An yi yunƙurin juyin mulki a Chadi

A ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu, an ji karar harbe-harbe a kusa da hedkwatar jam'iyyarsa a N'Djamena, babban birnin kasar.

Nova News ta bayyana hakan a matsayin yunƙurin juyin mulki.

Hotunan da ke yawo a shafukan sada zumunta sun nuna dimbin dakarun soji a titunan babban birnin ƙasar, da kuma motoci masu sulke da tankokin yaƙi.

Dillo dai babban abokin adawar ɗan uwansa ne, Shugaba Mahamat Deby, wanda ke kan karagar mulki tun shekarar 2021.

Abderaman Koulamallah, ministan sadarwa na ƙasar Chadi, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, niyyar da suka yi tun da farko ba ta kashe Dillo ba ce.

Kara karanta wannan

Binance: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya goyi bayan matakin da Shugaba Tinubu ya dauka

A kalamansa:

"Ba ya so ya miƙa wuya kuma ya harbi jami'an tsaro."

Ga hotuna da bidiyo a nan ƙasa:

Yunƙurin Juyin Mulki a Burkina Faso

A wani labarin kuma, kun ji cewa sojojin da ke mulki a Burkina Faso sun sanar da cewa an yi yunƙurin sake yin juyin mulki a ƙasar.

Sojojin sun bayyana cewa ɓangaren wasu sojoji ne ya yi yunƙurin kifar da Kyaftin Ibrahima Traore daga kan mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel