Shahararrun Musulman Duniya 500 a 2024: Tinubu, Dangote, Sanusi, Da Yan Najeriya 12 Sun Samu Shiga

Shahararrun Musulman Duniya 500 a 2024: Tinubu, Dangote, Sanusi, Da Yan Najeriya 12 Sun Samu Shiga

An lissafa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a matsayin daya daga cikin shahararrun Musulman duniya 500 masu fada a ji a 2024.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

An lissafa Shugaban Najeriyan tare da Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, Sultan na Sakkwato, Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano da wasu shahararrun musulman Najeriya 12.

Tinubu da Sanusi sun shiga jerin shararrun musulman duniya
Shahararrun Musulman Duniya 500 a 2024: Tinubu, Dangote, Sanusi, Da Yan Najeriya 12 Sun Samu Shiga Hoto: @GovKaduna, @officialABAT
Asali: Twitter

Cibiyar Nazarin Dabarun Musulunci ta Masarautar, Amman, Jordan tana wallafa sunayen manyan musulman duniya mafi tasiri 500 duk shekara.

Legit Hausa ta lura cewa Tinubu, wanda ya kama aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya a farkon shekarar nan, ya samu shiga littafin na shekara-shekara. Sai dai kuma, magabacinsa, Muhammadu Buhari, wanda ke yawan shiga wallafar baya, bai samu shiga wannan ba, yayin da Sultan na Sakkwato ya kama kambunsa a manyan shahararru 50.

Shahararrun Musulmai 500 na duniya a 2024: Cikakkun sunayen yan Najeriya a jerin.

Kara karanta wannan

Karar zabe da shari’a 5 da Abba Gida Gida ya rasa a wata 6 da zama Gwamnan Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

  1. Shugaban kasa Bola Tinubu
  2. Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, Sultan na Sakkwato
  3. Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Kano
  4. Alhaji Sanusi Lamido Sanusi, Sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Tijaniyah
  5. Farfesa Ishaq Olanrewaju Oloyede, babban sakataren kungiyar NSCIA kuma shugaban JAMB
  6. Sheikh Abdur-Rahman Ahmad, Jakadan kasa kuma Babban Limamin kungiyar Ansar Ud-Deen na Najeriya
  7. Sheikh Ibraheem Zakzaky, shugaban kungiyar yan uwa Musulmai na shi'a
  8. Sheikh Tahir Usman Bauchi
  9. Imam Muhammad Ashafa
  10. HE Ibrahim Saleh Al-Hussaini
  11. Sheikh Yakubu Musa Katsina
  12. Sheikh Farfesa Ibrahim Ahmad Maqari.
  13. Marigayi Prince Ajibola Bola
  14. Ibrahim Saleh Al-Hussaini
  15. Alhaji Aliko Dangote

A Najeriyam Shugaban kasa Tinubu, a matsayinsa na sabon shiga a jerin, ya kasance a karkashin shugaban siyasa.

A halin da ake ciki, Alhaji Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanonin Dangote, shine dan Najeriya da ya samu shiga a rukunin yan kasuwa, inda yake matsayi na 162 a matsayin daya daga cikin shugabannin Musulunci mafi shahara.

Kara karanta wannan

An maka shugaba Tinubu a kotu saboda wani dalili 1 tak

An tuna da Marigayi Prince Ajibola Bola, tsohon Alkalin Kotun Duniya da ke Hague, wanda ya rasu a ranar 9 ga Afrilu, 2023, a wani sashi na wallafar.

An shawarci Atiku da Obi kan batun shari'a da Tinubu

A wani labari na daban, Joe Igbokwe, jigon jam'iyyar APC mai mulki, ya shawarci Atiku Abubakar da Peter Obi a ranar Alhamis, 12 ga watan Oktoba, cewa su fara shirin zaben 2031.

Legit Hausa ta rahoto cewa da wannan furuci ba Ibokwe, yana nufin cewa Shugaban kasa Bola Tinubu zai yi kaka-gida a fadar shugaban kasa na cikakkun shekaru takwas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel